Tuesday, 24 September 2019
Zaman Me Jaruma Sadiya Adamu Take Yi A Otal Din Ni'ima

Home Zaman Me Jaruma Sadiya Adamu Take Yi A Otal Din Ni'ima
Ku Tura A Social MediaDuk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

To bayan mutuwar auren fitacciyar jaruma Sadiya Adamu yau kusan watanni takwas kenan ta tare a Otal din Ni'ima dake Kanon Dabo inda wasu ma suke cewa a cikin Otal din ta yi zaman iddar auren.

domin kuwa tun da auren ya mutu ta dawo ta tare a wajen ta zamar da Otal din nan ne wajen wuni kuma wajen kwana domin kuwa duk inda ta yi tafiya idan ta dawo to ba ta da wajen sauka sai Otal din Kuma ko da neman ta ake yi babu inda za a je a same ta in ba a Otal din Ni'ima ba.

Abin tun ba ya damun kawayen ta har ya zo yana damun su, hakan ta sa wasu daga cikin kawayen ta suka yi ta yi mata magana a kan rashin dacewar hakan amma jarumar ko a jikin ta.

A yanzu dai duk wani Sammakon ka in kaje Otal din za ka iya cin karo da ita, haka ma duk daren da ka yi za ka iya samun ta don haka duk wasu da suke ganin sun isa da ita sun yi mata magana amma ko a jikin ta don haka suka yi watsi da ita.

Saboda irin ci gaba na mai hakar rijiya da Sadiya Adamu ta samu, a yanzu tsohon yaron ta Wanda a baya kafin ta yi aure shi ne take aika ya sayo mata shisha da sauran kayan bukatu a yanzu Sadiya Adamu da shi take soyayya kuma an ce ta kamu da son sa sosai har ma ba ta jin maganar kowa idan ba ta sa ba.

Me za Ku Ce?

Share this


Author: verified_user

0 Comments: