Wednesday, 4 September 2019
Zaben Fidda Gwanin Gwamna A Kogi , Yan Bindiga Sun Bude Wuta

Home Zaben Fidda Gwanin Gwamna A Kogi , Yan Bindiga Sun Bude Wuta
Ku Tura A Social Media
Daga: jaridar dimokuraɗiyyar

An samu  harbe-harben bindigogi a safiyar yau a wurin taron fidda gwani na jam'iyar  PDP  wanda ya kai ga kawo karshen gasar.

Yunkurin da Sanata Dino Melaye ya yi na shiga takarar gwamna a baya ya kawo cikas ga gwamna Yahaya Bello.

A yanzu haka  bangaren jama'a tuni suka raja'a kan Sanata Dino Melaye, Sanatan yana barazanar kayar da gwamna Bello tare da dukkan karfin da zai iya kayar da shi.

Maharan sun yi ta rera yare daban-daban kuma suna kiran Dino Melaye da ya fita a wajen.

Mai magana da yawun Dino Melaye ya tabbatar da cewa Melaye ya samu munanan raunuka harbi a wurin taron amma yanzu yana karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Har yanzu dai likitoci suna ta kokarin ganin sun ceto rayuwarshi.

A garemu, zabe ba yaki bane amma tsari ne wanda ake baiwa mutane damar yanke hukuncin waɗanda zasu tafiyar da al'amuransu cikin yarda.

Don haka, muna kira ga dukkan masu goyon bayanmu a fadin jihar da su kasance masu bin doka da oda, su mayar da hankali da jajircewa kamar yadda haske zai mamaye duhu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: