Kannywood

Zaben AFMAN Na Kano Yabar Baya Da kura

A watan jiya ne aka gudanar da zaben Kungiyar Masu Hada Fina-Finai ta Arewa ta Kasa (Arewa Film Makers Association of Nigeria – AFMAN), inda Jamilu Yakasai ya zama Shugaban Kungiyar bayan ya doke abokin takararsa Abdallah Alkinana da Rashida Adamu, sai Lawal Ahmad ya zama Mataimakin Shugaba, Hannatu Bashir ta zama Sakatariyar Kudi, sannan Jamilu Roja Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar da sauransu.
Kwanaki bayan zaben, an gano wani faifan bidiyo na Jaruma Teema Makamashi tana cewa, “Na zabi Jamilu Yakasai, na zabi Lawal Ahmad, na zabi Hannatu Bashir. Wannan ra’ayina ne, saura inji wadansu kananan maganganu.”
Haka jim kadan bayan sanar da sakamakon, Sarki Ali Nuhu ya taya sababbin zababbun shugabannin murna, inda ya rika sanya hotunansu daya baya daya a shafinsa na Instagram yana taya murnar samun nasara, su kuma suna mayar masa da godiya.
Bayan nan, sai ga Mataimakin Shugaban, Lawal Ahmad ya wallafa wani sako a shafinsa na Instagram, “Allah Ya albarkaci wannan masana’anta tamu ta Kannywood. Ba mu da wani alfahari da ya wuce Kannywood. Da fatan manya da kanana za su ba mu hadin kai insha Allah.
“Shugabanci, adalci, zumunci, tarbiyya, sasanci, hadin kai, mu’amala, a gudu tare a tsira tare su ne insha Allah abubuwa kadan da za mu kalla a cikin wannan masana’anta tamu ta Kannywood.”
Sannan ya kara da cewa, “Wannan sako ne daga bakin shugabanni Kungiyar Arewa Film Makers Association Kano Chapter (AFMAN). Sako daga P.R.O”
A takaice suna kira ne ga sauran ’ya’yan Kannywood su hada kai da su domin gudanar da ayyyukansu.
Ba mu amince da zaben ba – Daraktan Kamfe na Alkinana
A wani gefen kuma, an jiyo wadansu suna cece-kuce da nuna rashin jin dadinsu kan yadda aka gudanar da zaben.
Daga cikin wadanda suka nuna rashin jin dadinsu, an jiyo Darakta Kamal S. Alkali wanda yake bangaren Alkinana yana cewa bai gamsu da zaben ba, inda ya yi zargin an tafka magudi a zaben wanda hakan ya sa ba za su amince da samakamakon ba.
Kamal ya ce za su je kotu domin neman hakkinsu, inda ya kara da cewa dan takararsa ya yi tafiya, amma da zarar ya dawo za su dauki mataki na gaba.
Na gamsu da zaben – Rashida Mai Sa’a
A nata bangaren kuma, mace tilo da ta tsaya takarar shugabancin kungiyar, Hajiya Rashida Adamu wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa’a ta bayyana cewa ta gamsu kuma ta amince da sakamakon zaben. “Na gamsu kuma na amince da sakamakon zaben. Sai dai kawai in yi musu fatan alheri,” inji Rashida Adamu.
Source: aminiyahausa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button