Friday, 27 September 2019
Video : Kalli Bidiyon Dangote Yana Tika Rawa Tare Da fitacciyar Mawakiya Teni A Amurka

Home Video : Kalli Bidiyon Dangote Yana Tika Rawa Tare Da fitacciyar Mawakiya Teni A Amurka
Ku Tura A Social Media
Abokanai, 'yan uwa da abokan arzikin attajirin da yafi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote sun shirya masa 'yar kwarya-kwaryar liyafa a cikin wannan makon bayan kammala kaddamar da Cibiyar Afirka wato 'Afirca Centre' a birnin New York a Amurka.

Attajiran duniya kamar su Bill Gates da Mo Ibrahim suma sun hallarci taron na kaddamar da cibiyar Afirkan.

A wurin bikin da aka shirya don karrama shi, an gano attajirin yana taka rawar 'zanku' tare da diyarsa Fatima yayin da wata fitacciyar mawakiya mai suna Teni ke rera masa wakarta mai taken 'Case' wadda dama ta ambaci sunansa da a cikin wakar.


Mawakiyar tana daya daga cikin masu kaunar Dangote hakan ma yasa ta ambaci sunansa a wakar ta.

Ga dai bidiyon yadda Dangote da diyarsa suka cashe tare da Teni kamar yadda The Nation ta wallafa.
Mutane da dama suna ta bayyana ra'ayoyinsu kan bidiyon na Aliko Dangote yana taka rawa da diyarsa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: