Saturday, 28 September 2019
Tuna baya: Jerin sunaye Da Hotunan Jaruman Nollywood mata Da suka Bar Addinin Kiristanci suka Dawo Musulunci

Home Tuna baya: Jerin sunaye Da Hotunan Jaruman Nollywood mata Da suka Bar Addinin Kiristanci suka Dawo Musulunci
Ku Tura A Social Media
Da yawa daga cikin jaruman fina-finai na kudancin Najeriya na Nollywood mata sun canja addini daga Kiristanci suka dawo addinin Musulunci. Wadannan jarumai mata dai duka suna da dalilansu na barin addinin Kiristancin suka dawo Musulunci

Ga jerin jaruman dai mun samo muku guda biyar daga cikinsu da kuma hotunan su:

1. Vivian Metchie


Vivian Metchie
Vivian ta bayyana cewa ta canja addini ne saboda a lokuta da dama tana shiga rudani saboda ganin yadda kiristoci suke sukan junansu haka kawai babu gaira babu dalili. Da take bayani akan dalilinta na barin addinin ta ce: "Ni na yanke hukuncin bari da kaina, nafi fuskantar Al-Qur'ani fiye da Bible, saboda haka ina bukatar salama da aminci, kuma na samu a cikin Al-Qur'ani.

Vivian ta canja sunanta daga Vivian zuwa Fareedah, a cewarta kuma iyayenta suna goyon bayan komowarta addinin Musuluncin.


2. Liz Da Silva


Liz Da Silva
Fitacciyar jarumar, Liz Da Silva kowa ya san cewa ita Kirista ce har sai lokacin da ta haihu da tsohon shugaban NURTW, Musiliu Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluomo.

A lokacin da suka samu sabani tsakaninsu, sai ta auri wani Musulmi mai suna Olaoye.

Saboda haihuwar danta mai suna Roheem da kuma sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta a ciki, Liz ta koma Musulma ta kuma canja sunanta daga Liz ta koma Aishat.

3. Lizzy Anjorin


Lizzy Anjorin
Lizzy ta taso cikin addinin Kiristanci ne, domin kuwa duka 'yan danginsu Kiristoci ne, amma sai Allah ya shiryeta ta dawo Musulunci.

A shekarar 2013, ta fito a fili ta sanar da duniya cewa ta koma addinin Musulunci, bata jima da bada wannan sanarwa ba kuwa ta tafi kasar Saudiyya domin sauke farali.

4. Laide Bakare


Laide Bakare

Laide Bakare Kirista ce har sai lokacin da ta rabu da mijinta, ta kuma fara soyayya da wani hamshakin mai kudi dake jihar Legas Alhaji Tunde Orilowo, wanda aka fi sani da ATM. Laide ta koma addinin Musulunci bayan ta aure shi inda ta shiga cikin jerin matanshi.

5. Lola Alao


Lola Alao
Jaruma Lola Alao ta Musulunta a shekarar 2016 inda hakan ya baiwa mutane da dama mamaki. Alao Kiristace dai kafin ta dawo addinin Musulunci. Alao ta koma addinin Musulunci jim kadan da mutuwar mahaifinta wanda yake shi ma Musulmi ne. Ta canja sunanta zuwa Rohdiat.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: