Labarai

Ta’addanci: Sojoji Da ‘Yan Siyasa Na Da Hannu Dumu-Dumu – Naja’atu Muhammad

An bayyana tabarbarewar tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya musamman yankin Arewacin kasar, a matsayin wata manakisa daga bangaren ‘yan siyasa da Soji wadanda suke azurta kan su da makudan kudade da gwamnati ke warewa domin yakar ta’addanci a Najeriya.

Jawabin haka ya fito ne daga bakin sananniyar ‘yar siyasa daga Kano Hajiya Naja’atu Muhammad, a yayin jawabin da ta gabatar mai taken “Ta’addanci da hanyoyin magance su a Najeriya” a taron da wata kungiya ta kasa da kasa ta shirya domin magance ta’adda a Najeriya wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja.

Naja’atu Muhammad ta cigaba da cewar, babu shakkar cewa Boko Haram ta samo asali ne daga jihar Borno, kuma ba kowa ya kirkiro kungiyar ba sai tsohon Gwamna Ali Modu Sheriff, kowa ya shaida cewa shi ya rene su har mukamin kwamishina ya bai wa daya daga cikin su, a yau Boko Haram sun addabi kowa, sannan shi Modu Sheriff na yawon sa a bayan kasa hankali kwance.

‘Yar Siyasar ta kuma soki lamirin rundunar Sojin Najeriya, inda suka mayar da batun tsaro ya zama wata hanya ta azurta kai, a lokacin Jonathan a na kashe Miliyoyin Daloli na Amurka a kowane wata da nufin samar da tsaro a yankin Maiduguri, amma babu abin da ya sauya, haka a gwamnatin Buhari aka sake ribanya wadannan kudade amma babu wani cigaban azo a gani da aka samu, da gangan sojoji suke jan kafa domin su samu kudi.

Hajiya Naja’atu Muhammad ta yi tir gami da Allah wadai da dabi’ar da sojoji suka rika yi a yankin Arewa maso Gabas, inda suka rinka aikata fyade ga ‘yan Mata har da Matan aure, babu wani gida a Maiduguri face sojoji sun aikata fyade a cikin sa.

Daga karshe ta bayyana cewar abu ne mai wahalar gaske a samu nasarar da ake nema ta yaki da ta’addanci, saboda wadanda aka dora wa nauyin yakin suke cin duddugen tsarin, sai dai gyaran Allah kawai.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button