Friday, 20 September 2019
Shin ko Kusan Dalilin Da Yasa Jaruma Jamila Nagudu Ta Kawo Wannnan Matsayi ?

Home Shin ko Kusan Dalilin Da Yasa Jaruma Jamila Nagudu Ta Kawo Wannnan Matsayi ?
Ku Tura A Social Media
Fitattaciyar jaruma Jamila Umar Nagudu ta yi ikirarin cewar biyayya da ta yi wa jagoriri a masana’anta fim shi ne ya kawo ta matsayin da take kai yanzu, saboda haka take kira ga sabbin jarumai mata da su kasance masu biyayya domin shi ne kadai abinda zai kai su ga gaci.

Jarimar ta yi wannan bayani ne a offishin Hukumar Tace Finafinai da yanzu haka ake tantance jarumai, inda ta je aka tantance ta.

Jamila Nagudu ta ce, “kusan shekara goma sha bakwai kenan ko ma fiye da haka ina wannan masana’anta, kuma kullum ana ci gaba da damawa da ni, wanda biyayya ce ta kai ta ga haka, domin ina zaune da kowa lafiay, ina bin kowa sau da kafa, tsakanina da shugabanni biyayya ce yayin da kuma abokan aikina mutunta juna ne.”

Sannan ta qara da cewar duk wadda za ta shigo sana'ar fim to ta mutunta iyayenta, 'yan uwanta da kuma abokan arziki da abokan aikinta sannan kuma shugabanninta.

Jarumar ta kuma jaddadawa tare da bawa sabbin jaruman shawara kan su zama masu biyayya ga wadanda suka samu, sannan su kasance masu hakuri da dauke kai, ba komai aka yi musu su ce za su dauki zafi ba, hakuri shi ne mataki na farko na nasara, sai biyayya don duk inda aka ce babu wadannan to babu nasara kuma babu daraja.

“Biyayya da hakuri sune mafita don koda mutum yayi niyyar yi maka wani abu na cin mutunci ko cin zarafi, da an tuna tana da hankali sai a daga mata kafa.” In ji jarumar.

Share this


Author: verified_user

2 comments: