Thursday, 12 September 2019
Shin Da Gaske : Hukumar Tace Finafinai Ta Jihar Kano Ta Kama Mawaki Nazir M. Ahmad ?

Home Shin Da Gaske : Hukumar Tace Finafinai Ta Jihar Kano Ta Kama Mawaki Nazir M. Ahmad ?
Ku Tura A Social Media

Daga Aliyu Ahmad

Rahotanni daga jihar Kano sun tabbatar da cewa hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta kama mawaki Nazir M. Ahamd bisa zargin sa da sakin wata wakar da hukumar ba ta tantance ba.

Majiyar ta bayyana cewa wakar da aka kama mawaki Naziru saboda ita, ta kai kimanin shekara uku zuwa hudu da sakinta.

Saidai wasu na ganin kamun da aka yi wa Sarkin mawakan na Sarkin Kano, ba ya rasa nasaba da wata talla da ya yi wa dan takarar gwamnan Kano karkashin PDP, Abba Kabir Yusuf.

Ku kasance da shin Hausaloaded.com zasuyi bincike sosai domin sanin sahihancin wannan labari a koda yaushe.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: