Friday, 20 September 2019
Sabon Cajin Banki, fashi da makami ne – Hon Kazaure

Home Sabon Cajin Banki, fashi da makami ne – Hon Kazaure
Ku Tura A Social Media
Hon Muhammad Gudaji Kazaure, dan majalissar tarayya mai wakiltar Gwiwa, Kazaure, Roni, Yan kwashi na jihar Jigawa, ya bayyana sabon tsarin carjin kudi na bankin CBN a matsayin fashi da makami.

Hakan na zuwa ne bayan da babban bankin CBN ta fitar da sanarwar fara daukar kudi a wajen masu asusun banki, a hada-hadar N500,000.Gudaji ya bayyana furucin ne a yayin da zauren majlissar tarayya ke tattauna batun.

“Idan mukayi duba da irin tsananin wahala da ake ciki yanzu, zamu babban Bankin CBN yana kokari zama tamkar ‘Yan Fashi da makami.”

Hon Kazaure, yayi kira da cewa, yunkurin babban bankin, zai tilastawa mutane ajiye kudadensu a gida, wanda hakan kuma zai baiwa bata gari damar cigaba da yin sace-sace a gidan mutane.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: