Monday, 16 September 2019
Rashin gaskiya ne ya hana aikin wuta a Mambila'

Home Rashin gaskiya ne ya hana aikin wuta a Mambila'
Ku Tura A Social Media


Sabon ministan lantarkin Najeriya Injiniya Sale Mamman ya ce ''sai nan gaba ne za a fara aikin wutar Mambila a jihar Taraba,'' sabanin maganganun da ake yi a baya cewa aiki ya yi nisa.
A hirarsa da BBC, ministan ya ce sabani tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kamfanonin rarraba wutar lantarki na daya daga cikin abubuwan da suka janyo tsaiko wajen aikin samar da wutar lantarki a kasar.
Ministan ya ce harkar wuta a Najeriya babba ce, domin tun yana karamin yaro ya san cewa babu isassar wuta a kasar.
Ya ce babbar matsalar da ta dabaibaye fannin wutar lantarki ita ce matsalar cin hanci da rashawa inda ya ce cin amana da rashin gaskiya ne ya kara gurgunta harkar wutar lantarki a kasar.
Ministan ya bayyana cewa sau da yawa wasu za su zo su karbi kudi kamar za su yi aiki da gaske amma daga baya ba za a yi aikin ba sai a yi kwana da kudin.
Ya yi zargin cewa wasu daga cikin shugabannin baya sun saka san rai wajen aikin wutar lantarkin kasar, wanda hakan ya ja kasar ba ta samun isassar wutar lantarki.
Ministan ya fito fili ya bayyana cewa har yanzu ma ba a fara aikin wutar Mambilla ba domin babban abin da za a sa a gaba a halin yanzu shi ne a je a share filin da za a fara aikin, ya kuma ce nan da 'yan kwanaki kadan za a fara aikin .
Ya dai yi alkawarin cewa kafin shekarar 2023 za su samar da mega watts kusan dubu 20 yadda 'yan Najeriya za su samu isassar wutar lantarki.
A baya dai an sha yin irin wadannan alkawuran na samar da wutar lantarki ga 'yan Najeriyar sai dai haka bata cimma ruwa ba.
Matsalar karancin wutar lantarki a Najeriya na daya daga cikin manyan matsalolin da kasar ke fuskanta wanda hakan ya yi sanadiyar durkusar da dubban kamfanonin sarrafa kayayyaki.
Duk da cewa ana samun wuta jefi-jefi a kasar, duk da haka 'yan kasar na kokawa kan yadda suke sayan wutar lantarki da tsada.
Hakazalika hatta masu kananan sana'oi da ke bukatar wutar lantarki a koda yaushe na cikin amfani da janareto wanda hakan kuma ke sa al'amuransu komawa baya.
Haka a ma'aikatu ko asibitoci ma, a koda yaushe sai dai kaga ana amfani da inji.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: