Thursday, 26 September 2019
Me Ya Sa Masu Kare Sheik Pantami Ba Su Kare Sheik Gumi Da Malam Daurawa Ba A Lokacin Da Aka Ci Zarafinsu?

Home Me Ya Sa Masu Kare Sheik Pantami Ba Su Kare Sheik Gumi Da Malam Daurawa Ba A Lokacin Da Aka Ci Zarafinsu?
Ku Tura A Social Media
RA'AYI


Daga Sani Rogo Aikawa

Ko kadan ban goyi bayan cin zarafin mutum a siyasa ba. Koda jahili ne ballantana malami. Sannan ban ji dadin abinda wasu suka yiwa Malami Isa Pantami ba, duk da sun yi masa ne a matsayin rigar siyasa ba ta malumta ba.

Babban Abinda ya sa ni wannan rubutun ganin yadda da yawan mutane idan suka tashi rubutu babu abinda suke yi sai tsinuwa tare da tofin Allah ya tsine ga 'yan Kwankwasiyya, wannan tsinuwar babu inda za ta  Kuma ba za ta taba shafar wanda bai yi laifi ba.

A cikin kowacce jam'iyya da kuma kowacce siyasa akwai malami akwai jahili, akwai mutumin kirki akwai na banza, babu jam'iyyar da ba za ka samu wadannan ba.

Ina kiraga matasanmu akowacce jam'Iyya mu guji cin zarafin kowanne irin mutum saboda mutum yanada daraja da mutunci badaidai bane cin zarafin masu mutunci.

Sannan ina son mutanen da ba su sani ba su sani matukar ka shiga siyasa babu abinda ba za ka gani ba sai dai a yi hakuri.

Sannan su ma malamanmu su guji cin zarafin mutane, su guji saka rigar malumta suna fakewa da ita suna hawa munbari suna zagi gami da habaici ga mutumin da suka suka raba layi a siyasance. Wannan ba daidai ba ne koda kai malami ne to ba ka san matakin da za ka taka a gaba ba.

Naga hotunan yadda wasu suka yi wa malamin ihun ba ma yi. Gaskiya ban ji dadi ba, duk da na ga da yawan 'yan uwan 'yan Kwankwasiyyar ne suke kare shi tare da nuna rashin jin dadinsu ga abinda aka yi wa malamin.

Har yau har gobe Malam Pantami yana da dubunnan masoya a tsarin Kwankwasiyya tare da ganin darajarsa da kuma sauraren karatunsa.

A lokacin da aka yi wa Malam wannan abun Kwankwaso, ba ya wurin sannan bai san an yi ba, na tabbatar da cewar da a ce Kwankwaso na wurin sai ya ci mutuncin duk wadanda suka yi wa malamin haka koda a cikinsu da 'dan cikinsa.

Sannan wannan abun baka da tabbas ko 'yan Kwankwasiyya ne baki daya suka yi wannan abu saboda filin jirgi wuri ne na mutane da dama.

Da a ce ina wurin, kuma da a ce ina da hanyar ganin Malamin da yace Masa, Bai kamata yafito ba alokacinda yaga "Yan kwankwasiyyar afilin jirgin kamata yai yayi hakuri ya tsaya har su Gama indai ba tafiyar tazama Dole ba.

MAKIYAN KWANKWASO NE KADAI KE TSINUWA

Mafi yawancin masu tsinuwar nan, son zuciya ce tsagwaron ta tare da kin gaskiya, suna fakewa da rigar siyasa domin su ci zarafin Kwankwaso da Kwankwasiyyar.

Wallahil azeem Akwai wanda yake 'posting' yana zagin Kwankwaso tare da Kwankwasiyya, Wallahi sau uku ina sasanta shi da gyatumar sa yana yi mata rashin mutunci. Amma ya zo yana zagin mutane.

Da yawan masu tsinuwar da zagin suna yin jama'une tare da zagin jama'u, sun manta da cewar a tsakar gidan suma akwai 'yan Kwankwasiyyar, wani iyayensa ne ke Kwankwasiyyar, wani matarsa, wani 'ya'yansa, wani 'yayan abokinsa, wani kuma 'kannen sa ne ke Kwankwasiyyar, shin idan ka yi tsinuwa baki daya wa ka tsinewa kenan?

Sannan masu ikirarin kare darajar malamai kuna ina ga tambaya ta gare ku.

(1) Wani Gwamna ya taba shiga kafafen yada labarai ya zagi Malam Aminu Ibrahim Daurawa,  har ma ya ce da shi barawo mara gaskiya, shin me ya sa baku fito kun yi rubutu kun kare darajar Malam Daurawa ba? Ko shi Daurawa ba malamin addini bane?

(2) Kuna ina aka dinga zagi tare da tsinewa Dakta Gumi saboda ya fadi ra'ayinsa na siyasa?
Me ya sa baku fito kun kare shi ba? Ko kuwa shi ba malamin addini bane? Ko kuwa saboda ba ya cikin jam'iyyarku?

(3). Kuna ina lokacin da aka yi wa Kwankwaso ihun ba ma yi a jihar Kaduna a cikin Masallaci, amma kuka yi shiru?

Don Allah mu gayawa kan mu gaskiya, wannan tsinuwar da kuke yi wa Kwankwaso babu abinda za ta yi masa, ba za ta taba rage masa daraja da mutunci ba sai ma ta kara masa, saboda ba don Allah kuke yi ba kuna yi ne saboda An taba jam'iyyarku.

Sannan ina jan hankalin mu da cewar mu guji cin mutunci da keta alfarmar kowanne irin mutum ballantana malamanmu masu daraja da mutunci.

Don Allah mu dinga ajiye son zuciya da son rai, mu dinga kyautatawa junanmu zato.

Ubangiji ya kara hada kawunanmu ya taimaki musulunci da musulmai.

Dukkan abinda na fada ra'ayina ne ba na wani ba, idan na batawa wani rai ya yi hakuri shi ma ba laifi bane idan ya rubuta nasa ra'ayin.

Daga SANI ROGO AIKAWA, DALA KANO.
08082744019.
09039128518.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: