Thursday, 12 September 2019
Martanin Mawaki Abdallah Amdaz Akan Kama Sarkin waka Nazir M Ahmad

Home Martanin Mawaki Abdallah Amdaz Akan Kama Sarkin waka Nazir M Ahmad
Ku Tura A Social Media

To jama'a kunci gaba da bibiyar shafinmu Hausaloaded blog domin kawo muku martani da bayyani akan kama shahararren mawakin kuma sarki waka,shima dai Abdallah amdaz ja nashi jawabi


"Narasa ma abunda zance. 
Amma dai yakamata  mu sani babu burgewa, ko abin alfahari akan taba mutuntakar wani. Kuma yin hakan keta iyakokin Allah ne. #Akaramakallahu kana da banbanci da ragon gidanku wajen hankali,  shiyasa Allah baiyi maka  kaho ba, ballantana ace kayi karo ga duk wani abu daya dameka, Allah ya baka hankali da natijar gane gaskiya, ya baka kwakwalwa da cikakken tunanin gane abunda ya dace da Wanda bai dace ba, Dan haka kada kayi amfani da matsayin da Allah Ya baka, wajen musgunawa wasu. Annabi SAW yana Cewa ya Ubangiji duk Wanda kaba jan ragamar Al'ummata, ya saukaka musu Al'amuransu na rayuwa, Allah ka saukaka  masa, Idan kuma ya kuntata masu, ya Allah ka kuntata masa. Allah Ka kuntata masa,  Allah ka kuntata masa. 
Dan haka ina Jan hankalinka #Akaramakallahu kada kwadayin gidan da ba'a dauwama, ya rudeka ka tarawa kanka hakkokin bayin Allah a kanka, mafi girman musiba bawa ya tashi a ranar Alkiyama, a gaban Allah da hakkokin jama'a a Kansa. Wallahi babu ruwan Allah da matsayinka, babu ruwan Allah da siyasarka Ko jamiyyarka, Kai tsaye abunda yake na nagarta shi Allah yake kallo. Kuma gaskiya ne, yanzu na fahimci ba #akaramakallahun dana sani da bane, Wanda ke haba haba da burin kyautatawa mutane, tare da musu fatan alkairi, saina gane shi wannan yana da zafin zuciya, karancin hikima, tare da karfin iko gami da mulkin dake Rudarsa, to Amma ina son yasani Kannywood, tafi kaunar wancan nada din, domin zaman lafiyarsa da kowa, shiyasa a baya take masa kyakykyawan fata, tare da Murna sanda ya samu matsayin farko dana biyu,  domin kuwa suna kallon wanda yasan matsalarsu ne yasamu Matsayi, sai kuma gashi lokaci guda ya manta da fafutukar da sukai har suka tabbatar masa da wannan  matsayi, inason natuna masa lallai zama da kowa lafiya, da yin gyara cikin hikima, shi ne hanyar shugabanni managarta, yin amfani da karfin mulki kona hukuma, baya haifar da komai sai tawaye da kokarin fito na fito da dokokin kasa - Kamar dai yanzun haka.

@sarkin_wakar_san_kano فصبر صبرا جميل 
#freesarkinwaka."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: