Friday, 6 September 2019
KWANKWASO YA SHAWARCI BUHARI : Rufe Boda Ba Zai Bunkasa Harkar Noma Ba ----Inji Kwankwaso

Home KWANKWASO YA SHAWARCI BUHARI : Rufe Boda Ba Zai Bunkasa Harkar Noma Ba ----Inji Kwankwaso
Ku Tura A Social Media
DAGA KABIRU ADO MUHD

Tsohon gwamnan kano kuma tsohon sanata me wakiltar kano ta tsakiya injiya Dr Rabi'u Musa kwankwaso ya shawarci shugaba Buhari cewa rufe bodojin Nigeria ba zai bunkasa harkar noma ba, dawo da tallafin taki da gwamnati ta janye shine kadai zai iya bawa manoma damar bunkasa harkokin nomansu.

Kwankwaso ya ce kamata yayi gwamnatin tarayayya ta dawo da tallafin taki data cire tare da tallawa manona dake lungu da sako na cikin kasarnan da taki taga aiki da cikawa.

Yace manoma ba sa iya sayen taki cikin saukin farashi ta yaya za ai su iya wadata abunda zasu shuka da takin duba da irin kuncin rayuwar da al'ummar kasa suke ciki?

 Yace yadda ake cewa an tara makudan kudade a kasarnan to in haka ne Nigeria takai matsayin da za ta rabawa manomanta taki kyauta ba wai ma su saya ba.

Yace kamar yadda yan Nigeria suka cancanci a basu illimi kyauta ( free education) to haka manoman Nigeria suka cancanci a basu taki kyauta.

Yace rufe boda ba zai bunkasa harkar noma ba sedai ma ya kara kawo talaucin da zai sa a kasa samun kudin da za a sayo takin.

Yace yana shawartar gwamnati da ta bude boda kuma ta tallafawa manoma da wadataccen taki domin sun cancanci ayi musu hakan.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: