Thursday, 5 September 2019
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un : Allah ya yi wa sananniyar mai fassara Al-Qur'ani mai girma rasuwa

Home Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un : Allah ya yi wa sananniyar mai fassara Al-Qur'ani mai girma rasuwa
Ku Tura A Social Media


Valeria (Iman) Porkhova, sananniyar mai fassara Al-Qur'ani da yaren Rasha ta rasu - Ta rasu ne tana da shekaru 79 a duniya - Fassararta kadai ce wacce aka yi da ayoyi kuma manyan malaman musulunci na duniya suka aminta da ita Sananniyar mai fassara Al-Qur'ani da yaren Rasha, Valeria (Iman) Porkhova, ta rasu a Moscow tana da shekaru 79 a duniya.

 Kafafen yada labarai na Rasha sun ruwaito cewa ta rasu ne a ranar Litinin, 2 ga watan Satumba. Rahoton ya kara da cewa addu'ar tunawa da ita a ranar Laraba 4 ga watan Satumba a wani masallaci da ke Moscow.

An haifeta a shekarar 1949 a garin Tsarskoye Selo a kasar Rasha. Porokhova ta kammala karatunta a Moscow State Pedagogical Institute of Foreign Languages kuma tayi aikin koyarwa na shekaru 18. Daga baya ta koma aiki a Russian Academy of Natural Sciences.

A shekarar 1975, ta auri wani dan kasar Syria inda suka bar Moscow zuwa Damascus a 1981 inda ta amshi musulunci ta kuma sami sunanta na Iman. A kasar Syria ta fara aikin fassara Al-Qur'ani mai girma zuwa yaren kasar Rasha. Ta kammala fassarar a 1991. Rahoto ya nuna cewa fassararta ita kadai ce wacce aka yi da ayoyi kuma malaman musulunci na kasashe daban-daban da suka hada da jamhuriyar Soviet suka aminta da ita.

Allah Ya Jikanta Da Rahama

Share this


Author: verified_user

0 Comments: