Thursday, 5 September 2019
Illar Ƙarya A Addini Da Adabin Hausawa - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Home Illar Ƙarya A Addini Da Adabin Hausawa - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Ku Tura A Social Media

ALLAH TA'ALA YA HANA MU ƘARYA, MANZON ALLAH SAW YA JA KUNNEN MU AKAN ILLAR ƘARYA DA HATSARIN TA.
ƘARYA ITACE BAYAR DA LABARIN ABINDA BA'A YI BA, KO KUMA ƘARYA TA ABINDA AKAYI, KO MUTUM YA FAƊI ABINDA BAAYI BA KO YA ƘARYA TA ABINDA YA FARU,
ƘARYA TA KASU HUDU A ADDINI
NA ƊAYA, YIWA ALLAH ƘARYA, KO YIWA ANNNABI SAW ƘARYA.
NA BIYU, ƘARYATA WANI ABU DA YA TABBATA A ADDININANCE, WANDA YA WUCE, KO WANDA ZAIZO, KO WANDA AKE CIKI YANZU,
NA UKU, SHEDAR ZUR, A GABAN KOTU, MUTUM YACE YA JI KO YA GANI KO ANYI ALHAKIN BAAYI BA, KO KUMA YACE BA'A YI BA ALHALIN ANYI.
NA HUDU, YIWA WANI SHARRI DA ƘAGE DAMIN ƁATA MASA SUNA.
NA BIYAR YIN ƘARYA DOMIN WATA MASALAHA, TA WARWARE RIKICI TSAKANIN MASU GABA KO TSAKANIN MAAURATA KO A FILIN DAGA WAJAN MAKIDAR YAƘI.
A AL'ADAR BAHAUSHE YANA NUNA ƘYAMA MAI TSANANI DA TUR DA ALLAH- WADAN MAƘARYACI
KUMA ƘARYA TANA  ZUBARWA DA MUTUM ƘIMA DA DARAJA DA MATSAYI A TSAKANIN AL'UMMA.
WANNAN YASA ACIKIN ADABI NA  HAUSAWA AKWAI JAN HANKALI DA KUSHE ƘARYA MISALI :
ƘARYA FURE TAKE BATA ƳAƳA
RAMIN ƘARYA ƘURARRE NE.
MAI ƘARYA ƊAN WUTA
MAI ƘARYA KO A RUWA GUMI YAKE
ƘARYA ZAGIN ALLAH
A TSINE UWAR MAI ƘARYA
ƘARYAR KA TASHA ƘARYA.
DA MAKAMAMTANSU DA DAMA
ALLAH YA TSARE MU ILLAR ƘARYA.
RANAR YAƘI DA ƘARYA TA DUNIYA.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: