Saturday, 7 September 2019




Fim Ne Silar Chanzawar Rayuwata - Jaruma Amina Yola

Home Fim Ne Silar Chanzawar Rayuwata - Jaruma Amina Yola
Ku Tura A Social Media
Amina Yola wadda aka fi sani da Meenat Yola tana daya daga cikin jarumai mata da a yanzu tauraruwarta take haskawa. Ta yi fina-finai da dama duk da cewar ba wani lokaci mai tsawo ta dauka a masana’antar ba, domin jin ko wacece Amina Yola wakilin mu ya tattauna da ita don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatu.

To Assalamu alaikum ni dai suna na Amina Yola sai dai an fi sani na da Meenat Yola kuma ni ‘yar asalin jihar Adamawa ce amma na tashi a oyo a can na girma na yi karatuna duk a can kuma hakan ya faru ne sanadiyyar mahaifina soja ne kuma a can ya yi zaman aiki kuma a yanzu da ya bar aiki muka dawo arewa da zama kamar shekaru hudu kenan da suka wuce.

To ya ya aka yi kika samu kan ki a harkar fim.

Ni da man tun ina karama ina da sha’awar harkar, to bayan mun dawo arewa da zama sai kuma na nemi yadda za a yi na shiga harkar fim din.

To yaya aka yi kika samu kan ki a harkar fim?

Na samu shiga harkar fim ne ta dalilin wata kawata duk da yake dai ita ba ‘yar fim bace amma tana da alaka da ‘yan fim don haka sai ta kawo ni wajen sa daga nan na fara harkar fim.

Ko za ki fada mana fim din da kika fara yi?

To fim din da na fara yi dai shine “Wani Lokaci” kuma Ibrahim Bala shi ne daraktan fim din.

Ganin cewar shine fim din ki na farko, ko yaya kika ji kafin a fara?

To gaskiya da yake na sa kaina a kan harkar don haka ni ban ji wani abu ba, na san dai akwai wahala amma da yake ina son abin ban ji faduwar gaba ba.

Kin yi finafinai sun kai nawa?

E to, duk da dai ba zan iya kawo su duka ba saboda wadansu ba su fito ba, amma dai wadanda zan iya fadarsu a yanzu sune kamar ‘Wani Kauli, Gidan Kitso, Samun Duniya, Matar Bahaushe, Tuggu da dai sauransu.

A cikin finafinan da kika fito wanne kika fi so?

To gaskiya duk ina son su amma dai idan za a ce na fitar da guda daya to zan iya cewa fim din Tuggu saboda shi ne fim din da na fito a matsayin jaruma ba kamar sauran fina-finan ba da wasu nakan yi sina-sinai biyu ko uku.

Ta yaya za ki kwatanta rayuwarki ta baya da kuma ta yanzu?

A gaskiya na samu canjin rayuwa sosai domin ita harkar fim kamar wata makaranta take duk yadda ka zo da ilimin ka to sai ka sake wani sabon karatu na rayuwa sa boda irin jama’ar da masana’antar ta tara, don haka akwai darasi na rayuwa a cikin harkar fim.

Kafin ki shiga harkar fim, ya kike kallon masana’antar?

A yadda nake kallon ta da kuma yadda nake jin ta da akwai bambanci da a yanzu da nake ciki, ka san ita harka ta rayuwa a yadda kake kallon abu da yadda kake jinsa a wajen mutane ba lallai bane ya zama daya da yadda lamarin yake. Don haka na samu labarai da dama a game da ‘yan fim, amma da na zo sai na ga abin ba haka yake ba, kuma ni ma abin da nake tunani da na shigo sai na ga ba haka ya ke ba, don haka ana fada min ‘yan fim suna da girman kai, sai kuma da na zo cikin su na ga ba haka abin yake ba sannan kafin na fara fim ina tunanin yadda za a hadu da manyan jarumai kuma yaya zan gansu. To sai kuima na zo muna tare da su muna yin aiki tare to abin sai ya burgeni sosai.

Kin zama jaruma, burinki ya cika kenan?

To ka san shi buri na rayuwa yana da yawa, don haka ta wani bangaren zan iya cewa burina ya cika, amma dai a yanzu ina son na zama fitacciyar jaruma kamar yadda sauran jarumai suka shahara a duniya.

Bayan harkar fim ko kina yin wata harka ta kasuwanci?

Eh, gaskiya ina yi harkar kasauwanci na kaya kamar atamfa da takalma da sauran kayan bukata na mata, kai har ma na maza ina sayarwa.

Me kika dauki harkar fim?

To ni na dauki fim a matsayin sana’a, kuma ita sana’a mutum shi ne yake sarrafata yadda ya ga dama, idan ya so sai ya zama mutumin kirki kuma idan ya so sai ya zama mutumin banza.

Wace rana ce ba za ki taba mantawa da ita ba?

To ni dai ina ganin ranar da ba zan taba mantawa da ita ba ita ce ranar da aka fada min zan yi aikin fim din Tuggu domin ba zato ba tsammani sai kawai aka sanar da ni na fito gobe zamu je aiki kuma da na je aka saka ni a matsayin jarumar fi

Share this


Author: verified_user

0 Comments: