Thursday, 5 September 2019
Duniya A Adabin Hausawa - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Home Duniya A Adabin Hausawa - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Ku Tura A Social Media

KALMAR DUNIYA  KALMACE TA LARABCI,  WANDA TAKE NUFIN ƘASƘANTACCIYA,  MARA DARAJA, DA ƘIMA
BAHAUSHE YAYI AMFANI DA KALMAR DUNIYA ACIKIN KARIN MAGANA DA SALON ZANCE, WAJAN NUNA ,RASHIN SAKIN JIKI DA SHANTAKEWA DA DUNIYA, DA BUGA MISALAI ,WAJAN RASHIN TABBACIN DUNIYA DA GUSHEWAR TA. DA JAN HANKALI DA FADAKARWA CIKIN AZANCIN ZANCE. WANDA KE NUNA CEWA DUK WANI KARIN MAGANA DA KALMAR DUNIYA TA FITO A CIKI, YA NUNA BAYAN ZUWAN MUSULUNCI AKA KIRKIRI WANNAN KARIN MAGANAR. KO SABODA ANA JI MALAMAI A WAJAN TAFSIRI SUNA NUNA RASHIN TABBACIN DUNIYA, KO KUMA YAU DA GOBE ANGA DUNITA DA YADDA TAKE , GA WASU DAGA CIKIN KARIN MAGANA ACIKIN ADABIN HAUSA DA SUKE NUNA HAƘIƘANIN DUNIYA,  DA FATAN ZAMU SAMU ƘARIN KARIN MAGANA WANDA SUKA FARA DA KALMAR DUNIYA, A CIKIN ADABIN HAUSAWA

DUNIYA MAI YAYI.
DUNIYA BUDURWAR WAWA.
DUNIYA MAKARANTA CE
DUNIYA MAKWANTAR RIKICI
DUNIYA A BITA A SANNU
DUNIYA MAI BAN MAMAKI
DUNIYA BA TA RAGO BA CE
DUNIYA BA MATABBATA BA
DUNIYA GIDAN KASHE AHU
DUNIYA CE GASHI NAN GA TA.
DUNIYA MU BITA ASANNU DON MAI ƊAUKA TANA AJIYEWA CE .
DUNIYA  SAI DA KARATUN TA NUTSU.
DUNIYA MASAKIN KUNU DAN ADAM YA ƊANƊANA TA A HANKALI .
DUNIYA GIDAN HIRA
DUNIYA SHIGA DAKIN MOTA , SHIGA DA KAI FITOWA DA BAYA.
DUNIYA RUMFAR KARA .
DUNIYA DA WUYAR ZAMA.
DUNIYAR WASU ALJANNAR WASU.
DUNIYA DA DAƊI A KAN  BAR TA .
DUNIYA TAFI ƘARFIN BABU
DUNIYA KWALLON  MANGWARO CE.
DUNIYA RAWAR YAMMATA.
DUNIYA A IDO TAKE AN SAI DA UWA AN SAI KWALLI.
DUNIYA BIRGIMAR HANKAKA, KA GA BAKI KA GA FARI.
DUNIYA CE TAFI BAGARUWA IYA JIMA.
DUNIYA JUYI-JUYI KWAƊO YA FADA RUWAN ZAFI.
DUNIYA MAI ƊAUKA DA AJEWA.
DUNIYA UWAR RUFI KO BA KI SON MUTUM BA YA SANI.
DUNIYA  MAI IDO A TSAKAR KA , BA KI GANIN GABANKI.
DUNIYA INA ZAKI DA MU NE.
RANAR HAUSA TA DUNIYA,  ALLAH YA TSARE DA SHARRIN DUNIYA.
ALLAH KASA MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA.

Share this


Author: verified_user

1 comment:

  1. Ina matuƙar Jin daɗin sauke waƙoƙi a wannan shafin naku, Amma Gaskiya matsalata daku shine baku saka waƙokin mawaƙa irinsu,Murtala badamasi Mani, Mallam Yahya Makaho, Aminu ringim bagwai.

    ReplyDelete