Thursday, 19 September 2019
Dalilai Goma Wadanda Ka Iya Sawa Abba Gida Gida Yayi Nasara a Kotun Zabe

Home Dalilai Goma Wadanda Ka Iya Sawa Abba Gida Gida Yayi Nasara a Kotun Zabe
Ku Tura A Social Media


Daga Khadija Garba Sanusi

1. dokar INEC tace idan har an kammala Zabe a akwati aka Kirga baka bayyana sakamakon Zabe amma daga bisani aka samu wani ko wasu sun yaga sakamakon Zaben na Hanun INEC har sun farfasa akwatunan sun lalata Takardun Dangwale(Ballot paper) ta yadda baza a iya sake kirgasu ba to abunda wakilin INEC na wannan akwati  zaiyi shine a karbo kwafi-kwafi din sakamakon da aka bawa Wakilan Jam'iyyu(Agents) yayi amfani dashi wajen sake tattara sakamakon Zaben da aka yaga.

2. haka Idan aka samu wani ya sace sakamakon Zaben ko dai an nemi sakamakon an Rasa to abunda aka fada da farko shi Jam'in INEC zaiyi.

3. Idan Kuma an kammala Zabe ne Amma ba'a Kai ga kirka kuri'un ba sai aka samu wani ko wasu sun fasa akwatun sun lalata takarkun da akayi Dangwale ta yadda baza'a iya kidayasu ba  to abunda Jami'in INEC zaiyi shine  ya soke wannan Zaben ta Hanyar cike wani Form mai suna EC40G ya bawa ko wanne Agent na Jam'iyya kwafin wannan Form din, shi dama wannan Form an tanadeshi ne kawai domin soke zabe.

4. Kotun Kolin Najeriya tayi Hukunchin akan cewa Duk wata akwatin Zabe dake tashar  Zabe Kuma akayi Zaben aka Kirga kuri'u aka Rubuta sakamakon Zabe aka rabawa Agents na Jam'iyyu kwafi-kwafi na Zaben aka sanarwa da Al'ummar da sukayi Zabe a wannan akwati sakamanon zabensu  to babu wata Hukuma ko wani Mutum Shi kadai ko Gungun Mutane da suka Isa su soke wannan Zabe sai Kotu ita kadai take Da Hurumin soke wannan Zabe.

5. A dukkan shaidun da Abba,Ganduje,INEC da APC suka bayar su sama da 40 kowa acikinsu ya tabattarwa Kotu cewa lallai wancan Zabe na farko Wato na 9 ga wata anyishi Lamin lafiya Kuma an Fadi sakamakon Zabe a ko wacce akwatu an bawa Agents na Jam'iyyu da Jami'an tsaro kwafi kwafi na sakamakon Zaben sai Daga baya Hukumar Zabe ta INEC ta soke wasu akwatuna guda 207 ciki har da Mazabar Gama dungurungun mai akwatinan Zabe 62 sannan wannan sokewa ba'a Rumfar zabe (akwati) akayita ba sannan ba'a tashar Zabe akayita ba, ba'a Matakin Mazaba akayita ba har ila yau ba'a Matakin karamar hukuma akayita ba, anyi wannan sokewa ne a wurin tattara sakamakon Zabe na Jiha.

6. Shi kansa Wanda ya Jagoranci Zabe Mazabar Gama na farko wanda INEC ta tura yazo Kotu yakuma fadawa Kotun cewar lallai ya tabbatar da cewa anyi Zabe a Mazabar Gama Lamin lafiya babu wani rikici da akayi ko Over Voting  saboda a duk Jami'an da ya tura akwatinan Nan 62 dake mazabar gama babu wani Jami'i da ya kawo Masa Rahoton Hatsaniya ko Over Voting a akwatinsa sun kawo Masa sakamakon Zabe ya shigar yakuma saka hanu sannan Agents na Jam'iyyu suma sun saka  Hanu yabasu kwafi kwafi na sakamakon Zaben ya sanar da sakamakon Zaben  a Mazabar Har Video akayi a wurin bayan yabaro wurin yazo wurin tattara sakamako na karamar Hukumar Nasarawa aka samu wasu a wannan wuri suka  Tayar da hargitsi har suka yaga sakamakon Mazabar sa na Gama.

7. Abba Kabiru Yusif ya damkawa wannan Kotu gaba Daya sakamakon Zaben Farko da akayi na akwatina 207 din Nan Wanda aka bawa Agents dinsa da ya tura ko wacce akwatuna hakan na Kara tabbatarwa Kotu da Duniya cewar lallai wannan kwafi kwafi na sakamakon Zabe da Abba yabawa kotu shine ya nuna anyi Zabe a wadannan a akwatina 207 Kuma an Kirga an rubuta sakamako an bawa Jam'iyyu kwafi-kwafi Kenan babu Wanda ya Isa ya soke wancan Zabe sai Kotun.

8. shaidun da INEC ta gabatar guda 3 ciki har da Jami'in da ya tattara sakamakon Zabe na karamar Hukumar Nasarawa dukkansu sunce babu Wanda yayi shawara Dasu Kan maganar soke zabe Suma kwatsam sukaji an soke Zaben akwatina 207 daga cibiyar tattara sakamakon zabe ta jiha, sannan Lauyoyi sun Tambayesu ko shin Suna da masaniyar Over Voting da akace anyi Wanda shine silar soke wadancan akwatina, Shaidun sun fadawa Kotu cewa Suma haka sukaji Ana rade radi Amma babu wani Jami'in INEC da suka tura wata akwati Wanda yazo musu da Labarin anyi Over Voting ko Hargitsi a akwatinsa.

9.Lauyoyi Ganduje da INEC sun kasa gabatarwa Kotu Form din soke Zabe na akwatina 207 Wanda zai tabbatar da da'awarsu ta lallai waccan sokewa da akayi akan ka'ida yake kamar yadda Shi Abba ya gabatar da sakamakon zaben akayi a wadancan akwatina, wani abun mamaki ma shine a kokarin Lauyan Ganduje da yakeyi na gabatar da sakamakon wata akwati na karamar Hukumar Bichi sai ya gabatar da sakamon wata akwati a karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi sannan Lauyoyin Ganduje sun kawo wani shaida a Kotun Mai katin Zabe na Bogi, wadannan abubuwa Gudan biyu ba karamar kasawa bace ga Lauyoyin Ganduje.

10. da Lauyin Abba suka matsa akan lallai sai Lauyon INEC Dana Ganduje sun gabatar musu da Form din Soke na EC40G sai Lauyoyin na Ganduje suka gabatar da na akwati daya kacal maimakom su gabatar Dana akwatina 207 Shima wannan dayan an Rasa waye ya rubutashi, saboda akwai kura kurai da Yawa acikinsa musamman Bangaren kwanan wata.

Darajar Manzon Allah(SAW) da wadannan Dalilai ko  Hujjojin da muka zakulo da Kuma Addu'o'in Mutane muke sa ran In Allah ya yarda wannan Kotu Mai Albarka zata Bayyana Abba Kabir Yusif amatsayin Wanda ya Lashe Zaben Gwamnan a Jihar Kano na shekara ta 2019 da karfin Mulkin Allah. Domin har kullum muna fada ita Shari'a Abu 3 take Bukata Gaskiya,Hajjoji da Kuma Adalchin Alkalai, Alhamdulillahi Abba yanada biyu Wato Gaskiya da Kuma Hujjojin abunda ya rage kawai shine Adalchi Alkali Wanda wannan kuma ba hanunsa yake ba a Hanun su Alkalan yake kuma Insha'Allahu Muna da yakinin zasuyi Adalchin.
Allah yacigaba da bamu Nasara Alfarmar Manzon Allah(SAW)


Share this


Author: verified_user

0 Comments: