Labarai

Dahiru Bauchi Ya Yi karin Haske Game Da Harbe Harbe Da Aka Yi A Gidansa

Fitaccen Malamin addinin Musuluncin, kuma jagoran darikar Tijjaniyyah, Shehi Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa harben harben da aka yi a gidansa dake Bauchi da har ya sabbaba raunata wasu mutane biyu ya faru ne sakamakon rashin jituwa da aka samu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Shehin Malamin ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Satumba yayin da yake ganawa da jama’a a gidansa, inda yace rashin jituwar kuwa ta auku ne tsakanin Yansandan dake gadin gidansa da kuma wani bako da ya yi kokarin shiga gidan.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dahiru Bauchi yana cewa: “Da wannan mutumi ya nemi ya shiga gidana sai Yansandan dake gadi suka hana shi shiga sakamakon basu gamsu da shi ba, wannan ne ya kawo cacar baki tsakaninsu, har Yansandan suka yi harbi domin su tsorata mutumin.


“A dalilin haka suka ji ma mutane biyu rauni, a yanzu haka mutum daya na asibiti yana samun kulawa, yayin da dayan kuwa har ma an sallameshi.” Inji shi.

Shehin Malamin ya tabbatar da cewa doka ta baiwa Yansandan daman harba bindiga domin su tsoratar da duk mutumin da ya ki yin biyayya ga umarninsu, sa’annan ya gargadi masu watsa jita jita da su daina, domin kuwa babu wanda ya kai masa hari.

A wani labarin kuma, akalla dakarun Sojin Najeriya guda 20 dake aikin tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso gabas a karkashin Operation Lafiya Dole ne suka yi batan dabo bayan wani hari da mayakan Boko Haram suka kai ma Sojoji a Borno.

Baya ga bacewar Sojoji 20, an tsinci gawarwakin wasu Sojoji guda 9 bayan harin da yan ta’addan suka kai musu a kauyen Granda dake cikin yankin Gudumbali na jahar Borno.

Yan Boko Haram sun shirya harin kwantaun bauna ne a kan sansanin Sojojin Najeriya a daidai kauyen Granda da tsakar daren Litinin, inda aka yi ta musayar wuta har zuwa safiyar Talata, 10 ga watan Satumba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *Back to top button