Kannywood

Bollywood Ta Koyi Abubuwa Da Dama Daga Kannywood – Darakta Aminu S Bono

Babban daraktan finafinan Hausa, Amisu S Bono, ya ce akwai abubuwa masu yawan gaske da masana’antar shirya finafinan Indiya ta Bollywood ta kwaikwaya daga Kannywood, ciki har da hada manyan jarumai a wuri guda su yi waka.
Daraktan ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Freedom da ke Kano, inda ya ce hadin kai da ‘ya’yan masana’antar fim din Hausa suka rika yi a baya shi ne babban dalilin da ya bata nasara a wancan lokaci, yanzu kuma rashin hadin kai ne yake sanya lamura tabarbarewa.
Aminu S Bono, wanda ya bada umarni a finafinai da wakoki masu yawan gaske, ya nuna takaicinsa kan yadda harkokin suke tafiya yanzu.
Daraktan ya ce: “Lokacin da aka kafa Kannywood har aka nada mata wannan suna karkashin jagorancin marigani Sanusi Shehu Daneji, hadin kai ne yake tafiyar da ita. Shi ya sa ma aka rika samun finafinai da za a ga jarumai sama da 30 a cikinsa. Za a hadu a wuri guda, a yi komai tare. Babu wanda yake yi wa wani kyashi ko bakin ciki.”
Aminu Bono ya bada misali da finafinai irinsu Tutar So, Harafin So da sauran su, da ya hada kusan dukkan manyan jaruman masana’antar, wanda daga nan Bollywood ta kasar Indiya ta kwaikwaya har ma aka yi irin wannan hadakar a wani fim din jarumi Shah Rukh Khan mai suna Om Shanti Om.

Da yake magana kan rashin tsari, Daraktan ya ce baragurbi ne da suka shigo cikin masana’antar suka lalata komai, musamman da yake ita Kannywood din ba kungiya ba ce mai rajista, shi ya sa kowa yake ganin yana da ikon bude shafuka da sunan Kannywood ya yi abinda ya ga dama.

Ya ce duk wanda ya san Kannywood a shekarun baya, masana’anta ce mai hadin kai da kauna juna, kowa yana mararin ganin dan uwansa.
“A shekarun baya za ka samu manya a masana’antar fim a wuri guda suna hira tare, kullum maganar ba ta wuce shirya fim, kowa yana kokarin ya yi gasa da abokin sana’arsa wajen shirya fim mai kyau, ba a da wata magana sai ta fim, amma yanzu agololi sun shigo, suna bude shafuka da suna Kannywood suna yada abubuwa marasa dadi.”

Matsalarmu guda daya ce, duk wanda ya shigo karbarsa kawai ake yi tare da sanin daga inda ya fito ba, wanda a baya kusan dukkan masu warkajami a har sun san junansu, kuma suna girmama juna.” A cewar daraktan.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

  1. Karya yake kar ya maida mutane jahilai mana yanaso yagayamana cewaar fina finan hausa sun riga na indiya ne farawa ma ana kannywood tariga bollywood ne? Karyar banza

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button