Friday, 6 September 2019
Ba Za Mu Ci Amanar Shugaba Buhari Ba, Cewar - ISheik sah Pantami

Home Ba Za Mu Ci Amanar Shugaba Buhari Ba, Cewar - ISheik sah Pantami
Ku Tura A Social Media


Ministan sadarwa na Nijeriya, Ash-sheikh Dr Isah Ali Ibrahim Pantami (H) yace: "Ba za mu taba cin amanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bamu ba".

Ministan ya ci gaba da cewa; "a matsayina na Maigirma Minista a Nigeria ba zan taba cin amanar shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba bisa amanar da ya bani, zanyi aiki tukuru ba dare ba rana tare da sauran shugabannin gudanarwa na ma'aikatar Sadarwa don ganin mun sauke nauyin amanar da shugaba Muhammadu Buhari ya daura mana".

Maigirma Ministan ya yi wannan jawabin ne a yau Alhamis 4-9-2019 a lokacin da ya karbi bakwancin wasu manyan wakilai daga Kasar Burtaniya karkashin jagorancin Miss Harriet Thompson

Wakilan Kasar Burtaniyan sun kawo masa ziyara ne domin su tayashi murnan mukamin da aka bashi, sannan suyi nazarin hanyoyin da za'abi wajen habbaka bangaren fasahar sadarwa na zamani a cikin Kasarmu Nigeria kafin Ministan ya tafi Kasar Ingila halartan wani taron nahiyar afirka da aka tsara za'a yi

Magirma Ministan ya kara da cewa Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsarawa dukkan ministocinshi abinda yake da burin su aiwatar a wannan wa'adin mulkinsa na biyu, a wannan karon shugaban kasa Buhari ba zai karbi uzuri na ganganci ba, munyi alkawari zamu habbaka harkan fasahar sadarwa na zamani anan gaba.."

Muna rokon Allah Ya yiwa Ministan sadarwa jagoranci, Allah Ka bashi ikon sauke nauyin shugabancinsa. Amin.

Daga Datti Assalafiy

Share this


Author: verified_user

0 Comments: