Thursday, 19 September 2019
Alherin Allah Ya Kai Ga Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami (karanta)

Home Alherin Allah Ya Kai Ga Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami (karanta)
Ku Tura A Social MediaMaigirma Ministan sadarwa na Kasarmu Nigeria Dr Isah Ali Ibrahim Pantami ya rubuta wasika zuwa ga Maigirma Ministan Ayyuka na Kasar Nigeria Babatunde Fashola yake tunatar dashi manyan ayyukan gina titi da ake yi a mahaifarsa na jihar Gombe kamar haka:

-Hanyar Gombe zuwa Potiskum
-Hanyar Gombe zuwa Biu
-Hanyar Gombe zuwa Dukku
-Hanyar Gombe da ta tashi zuwa Yola

Maigirma Ministan yayi kira ga takwaransa Ministan ayyuka da ya kai agajin gaggawa game da gyaran wadannan hanyoyi da sukeyin tafiyar hawainiya

Ina mutanen Gombe da suka nuna adawa da hassada lokacin da shugaba Buhari ya fitar da sunan Malam Isah Ali Pantami cikin wadanda zai basu mukamin minista?
To kunga kyakkyawan yunkurin da Malam yake yi domin cigaban jihar Gombe

Muna fata a nan gaba Gombawa zaku zabi Malam a matsayin gwamna

Yaa Allah Ka daukaka darajar Malam Isah Ali Ibrahim Pantami


Share this


Author: verified_user

0 Comments: