Kannywood

Zan kai Dana Turai Har sai Ya Zama Tamkar Ahmad Musa -Ali Nuhu

Daga Shuaibu Abdullahi

Rahotanni masu tushe sun bayyana cewar Jarumi Ali Nuhu ya ware makudan kudade wajen tura Yaron sa Ahmad, zuwa kasashen turai don ya goge a fagen kwallon kafa.

Rahotanni sun bayyana cewar Jarumi Ali Nuhu ya canza shawarar daya dauka na ganin Yaron nasa ya zama babban Jarumi a masanaantar Kannywood.

Haka kuma Jarumin yayi dubo da sanaar murza Kwallon kafa ta yadda take  chanza mutun zuwa babban matsayi a duniya, har ila yau Ali Nuhu yana mai son ganin Yaron sa ya zama Gwarzo kamar abokin sa Ahmad Musa, na Super Eagles.

Har ila yau rahotan daya zo a boye ya ce Ali Nuhu, ya shirya ci gaba da narka manyan kudade har sai ya cimma burin sa.

Sai dai masu bayyana raayoyi sun duba cewar Jarumi Ali Nuhu, yana mai kallon rayuwar abokin sa Ahmad Musa, da irin daular da kwallon kafa ta saka shi, nada nasaba da daukar matakin a kan Yaron sa.

Ya sami shawarwari da daurin gindi daga Dan wasa Ahmad Musa, kafin ya sami damar tura Yaron nasa zuwa Turai.

Da farko Ali Nuhu, ya sanya Yaron sa Ahmad a harkar Fina-finai, inda yaron ya fito a fina-finai da dama don har ya lashe lambobin Yabo.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button