Friday, 9 August 2019
Yadda Zaka Samu Kyautar N5000 A Layin MTN

Home Yadda Zaka Samu Kyautar N5000 A Layin MTN
Ku Tura A Social Media
Kamar dai yadda muka sani, dokar hukumar sadarwa ta kasa (NCC) ta bukaci duka masu amfani da wayoyin hannu da su yi ma layukan da suke amfani da su rajista ta hanyar bayar da bayanan kansu wadanda ake tattarawa a ma’ajiyar bayanai ta hukumar.
Kamfanonin layuka irinsu MTN, Airtel, GLO, Etisalat da sauransu sun cika wannan umarni ta hanyar samar da na’urori da gurabe da za’a rika gudanar da wannan rajista ga sabbi harma da na tsofaffin masu amfani da layukan wayoyin.
 
A yan kwanakin nan ne wasu daga cikin masu amfani da layukan MTN zasu rika gani wasu sakonni daga kamfanin akan suje su sake yin rajista ta hanyar kara bayar da bayanan da suka bada a yayin waccan rajistar ta baya kafin zuwa karshen watan August da muke ciki.
Y’ello! Kindly visit any MTN store with a valid government approved ID. Your SIM details need to be updated before August 19th. Dial *123*7*1# for the nearest store.
Da zarar ka karbi irin wancan sako dake sama sai kayi maza ka garzaya zuwa ofishin MTN ko kuma cibiyar rajistar layin waya dake kusa dakai don a sake maka sabuwar rajista.
Da zarar ka kammala, MTN zasu yo maka sakon cewa sun baka kyautar N5000 don biyanka wahalhalun da kayi wajen sake yima layinka rajista.
Abin lura:
Zaka iya amfani da kudin wajen kiran ko wanne irin layi, sannan kuma wadanda basu ji irin wannan sakon ba su jira suma zasu ji nasu..

Share this


Author: verified_user

0 Comments: