Kannywood

Yadda Ta Kaya Zaman Farko Na Shari’ah Censorship Board Da Sanusi oscar 442

Hukumar tace finafinai karkashin jagorancin Isma’ila Na’Abba Afakallahu, tana zargin Sunusi Oscar 442 da laifu kamar haka

•Ya saki wakar Hasashe (wadda yanzu haka kusan shekarar ta hudu da fita) ba tare da satifijet ba, wanda shi Oscar musanta laifin a gaban Kuliya. Domin ya ce ba shi ne ke da ikon fitar waka ba. Shi darakta ne.

•Akwai wakar Garzali Miko da aka dora a YouTube kwana baya (a kalla wata guda da ya ya wuce) ita ma wai ba yi censoring ba. Har ila yau Oscar ya musanta laifin, domin ya ce shi ko YouTube channel ba shi da ita. Saboda haka laifin da ake tuhumarsa bai aikata ba.

Lauyan Oscar ya yi iya bakin kokarinsa domin Alkali ya bada beli, hakan bai samu saboda Alkali ya dage shari’ar zuwa 20 ga watan nan da muke ciki.
Kafinka wasu sun hau kujerar kuma sun wuce.
Mun munsani zaka sauka kuma zaka girbi abinda ka aikata da yardar Allah. –

Daga kannywood paparazy

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button