Sunday, 25 August 2019
Yadda Musulmai Suka Koma Sallah A Waje Bayan Gwamna Wike Ya Rushe Musu Masallaci A Garin Fatakwat (Hotuna)

Home Yadda Musulmai Suka Koma Sallah A Waje Bayan Gwamna Wike Ya Rushe Musu Masallaci A Garin Fatakwat (Hotuna)
Ku Tura A Social Media

Daga Ibrahim M Abdullah

Masallanin da Wike ya rusa kenan sannan Shugabannin al'ummar musulmai a Port Harcourt, ta jihar Rivers sun yi Allah wadai da rusa babban Masallachin Juma'an dake Trans-Amadi.

Haka zalika sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Majalisar Kasa da su sanya baki dan baiwa kimanin Musulmi dubu goma dake yankin 'yancin gudanar da Ibadarsu ba tare da tsangwama ba.

Haroon Muhammed, shine Limamin wannan masallaci, ya ce wasu jami'an Gwamnati ne suka zo suka rusa masallacin, inda suka zo tare da jami'an 'yan sanda wato a ranar 20 ga watan August, 2019 a cewarsu wai ginin masallacin sabawa ka'idar gini ta jihar.

Haka nan sun yi roko ga Gwamna Wike, da ya sa baki akan wannan turka turka, Imam Muhammed yace: “muna kira ga duk al'ummar Musulmin duniya su shaida abunda ake mana. Wannan Masallachi Munsayeshi da kudin mu munbiya a Gwamnatin baya da ta gabata kuma ta Aminche mu gina.

Wannan shine karo na uku da ake yi mana barazana, na farko shine a ranar 29 na watan da ya gabata, sai kuma 16 ga watan Augusta sannan wannan na ranar 20 ga wannan watar! 20 ba tare da an ba mu wata sanarwa ba.

An hana mu wajen Ibada kuma an hana mu koka, muna son Duniya ta kalli abunda ake mana mu mutane ne masu bin doka da oda, har kotu mun je a cikin watan Nuwamban shekarar 2017 kuma kotu ta bamu damar mu amma kuma jami'an Gwamnati na cigaba da musguna mana".
Share this


Author: verified_user

0 Comments: