Saturday, 17 August 2019
Wata sabuwa : An Kama Sadiya Haruna

Home Wata sabuwa : An Kama Sadiya Haruna
Ku Tura A Social Media

A jiya ne jam'ian tsaron jihar Kano, suka cafke wata matashiya wadda ta yi kaurin suna wurin maganganu a shafin Instagram mai suna Sadiya Haruna.

Sadiya ta kware a wurin yin bidiyo na rawa tana dorawa a shafukan ta na yanar gizo, sannan kuma gwana ce wurin dauko maganganu kala-kala wadanda suka shafi mata da maza tana tsokaci a kan su.

A kwanakin baya ta fito ta bayyana wasu jaruman Finafinan Hausa a matsayin macuta wadanda suka zalunce ta a lokacin da ta yi aikin fim a shekarar da ta gabata, jaruman da ta lissafa a matsayin Macuta suna hada da Aminu A. Dagash, Alhassan Kwalle, da kuma Lawal Sa'idu Washasha

Ta kuma bayyana shugaban jarumai na Masana'antar Kannywood wato Alhassan Kwalle, a matsayin wanda ya nema ta da lalata ta ki yarda, wanda ta ce shi ne dalilin sa na gudowa daga Maiduguri wurin aikin ta ba tare da ya ida ba, saboda kin ba shi hadin kai da ta yi.

Sai dai daga baya shi Alhassan Kwalle da kuma Aminu A. Dagash sun fito sun wanke kan su ta hanyar yin magana wadda ta kai tsawon mintuna shidda suka rika turawa a dandalin sada zumunta na WhatsApp

Sadiya Haruna ta yi kaurin suna a Instagram inda ta samu yawan mabiya ta dalilin maganganu wadanda suka shafi rayuwar aure, wanda wasu suke ganin babu abin da ta ke yi illa batsa. Sannan a nan ne ta ke tallata hajar ta ta sayar da magungunan mata irin su man shafawa da sauran su.
Sai dai da yawa daga cikin mabiyan ta na alakanta ta da 'yar Kannywood. Wadda duk abubuwan da ta ke wasu na kallon ta a matsayin 'yar fim.

Wata majiya ta tabbatar wa kafar watsa labarai ta Kannywood Exclusive cewa ba za a sake ta ba, sai zuwa ranar Litinin, inda za a gindaya mata sharudda cikin su har da fitowa ta karyata kan ta tare da ba duk wani dan fim da ta taba zagi hakuri.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: