Friday, 23 August 2019
VIDEO: Kalli Bidiyon Maigirma Minista Yayi Kuka Da Zubar Da Hawaye

Home VIDEO: Kalli Bidiyon Maigirma Minista Yayi Kuka Da Zubar Da Hawaye
Ku Tura A Social MediaAllahu Akbar! Dazu a gurin walima da aka shirya wa Malam Isah Ali Pantami a Masallacin Annoor, bayan an bashi dama ya gabatar da jawabi, sai yace ba murna zaku tayani ba, akwai babban aiki da kalubale a gaban mu, da kuma amana da aka bamu.., kawai sai ya fashe da kuka, jawabin da bai karasa ba kenan
Wannan kalubale ne ga mahassada da suke cewa Malam yanzu kuka ya kare tunda ya zama minista, ko shekaran jiya ma sai da naga wani marar kunya yana fadin haka cewa Malam kuka ya kare.

Karfin imani da tausayi da tunanin lahira da tsoron Allah shi ke sa bawan Allah musulmi yayi kuka, mu a garemu wannan rahama ce.
Wannan shine karon farko a tarihin Nigeria da wani Minista ya zubar da hawaye saboda tsoron Allah akan girman amana da aka bashi
Yaa Allah Ka yi riko da hannun Malam, Ka masa jagoranci, Ka bashi nasaran sauke amanar da aka daura masa Amin

Ga bidiyon nan Kasa
Share this


Author: verified_user

1 comment:

  1. Allah ya kara ma mallam da sauran shugaban mu lafiya da imani da kuma illimin mulki da kuma yin addalci mana amin

    ReplyDelete