Friday, 9 August 2019
Miliyan N2 ne farashin kwanciya da ni kuma a haka 'yan Najeriya ke yi min layi kullum - Wata karuwa

Home Miliyan N2 ne farashin kwanciya da ni kuma a haka 'yan Najeriya ke yi min layi kullum - Wata karuwa
Ku Tura A Social Media
Toyin Lawani, wata fitacciyar mai zaman kan ta a jihar Legas ta bayyana cewa tana karbar miliyan biyu daga hannu duk wanda ke son kwanciya da ita.

Matar ta bayyana haka ne a matsayin martani ga sukar da wani jarumin wasan barkwanci, MC Jollof, ya yi mata a kan neman kudin da suka wuce kima ga masu son hulda ita.

Da take yi wa MC Jollof a kan ya fita daga harkokinta, Toyin ta bayyana cewa duk da tana karbar miliyan N2 kafin amincewa da abokan kasuwancinta, hakan bai hana maza yi mata layi ba.

Kazalika, ta kara jaddada cewa duk mai son ya kwanta da ita, dole ya shirya yin sallama da a kalla miliyan biyu daga aljihunsa.


A sakon martanin da ta wallafa a shafinta na sada zumunta (Instagram), Toyin ta rubuta cewa, "na yi maka kama da irin matan da zasu karbi dubu N100 a matsayin sallama bayan kwanciya da su? na fi karfin duk wani namiji da iya dubu N100 zai iya kashe wa a kan mace.

"Akwai wadanda ke bani miliyan biyu domin kawai mu fita tare, mu ci abinci. Akwai wadanda zasu iya bani miliyan N20 domin kawai na amince su kwanta da ni."

Majiyarmu ta samu wannan labari daga legithausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: