Kannywood

To fah: Abinda Nake Nema Ba Shi Na Gani Ba, Saboda Haka Na fita Daga Kannywood – Jaruma Halima Abdulkadir

Kyakkyawar jarumar fina-finan Hausa Halima Abdulkadir wacce aka fi sani da Intisar ta bayyana cewa karshen zamanta a masana’antar Kannywood ya zo

– Inda ta ce abinda ta zo nema a masana’antar ba shi ta samu ba, sannan kuma abinda ta yi tunani ba shi ta gani ba

– Ta ce ita tunda ta fara harkar fim ba ta taba samun matsala da kowa ba, kuma babu wanda ya taba samun matsala da ita

Wani bidiyo da ya dinga yawo a shafukan sada zumunta ya bayyana yadda kyakkyawar jaruma Halima Abdulkadir wacce aka fi sani da Intisar ta bayyana cewa ta fita kwata-kwata daga masana’antar Kannywood.

Ga dai abinda jarumar ta ce a cikin bidiyon:

Assalamu Alaikum jama’a suna na Halima Abdulkadir wacce aka fi sani da Intisar, ina so nayi amfani da wannan damar na sanar da jama’a da masoyana cewa daga ranar irin ta yau 29 ga watan Agustan shekarar 2019, ni ba ‘yar fim bace ba, na fita daga masana’antar Kannywood.”


“Kar mutane su dauka cewa wani abu ne marar kyau ya faru da ya sanya na fita, ba haka bane, tunda na shigo masana’antar nan ban taba samun wani tashin hankali da kowa ba, kawai dai wani daliline guda daya yasa na fita, abinda nayi tunanin zan gani a masana’antar ba shi na gani ba, abinda kuma nazo nema bashi na samu ba.

“Sannan ina rokon duk wanda na yiwa laifi ya yafe mini, nima kuma na yafewa kowa da kowa, na gode.”

Ga bidiyon nan  daga shafin ta


View this post on Instagram

A post shared by Halima Abdulkadir Adam (@inteesaar_elfallatah) on
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button