Labarai

Tirkashi: A wannan karon Zahra Buhari ta zo da wata zazzafar magana

‘Yar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta wallafa wata magana a shafinta na Instagram

– Ta wallafa yadda mutane za su kwantar da hankalinsu idan suna samun barazana ta takurawa ko cin zarafi daga wajen wasu

– Ta kuma gargadi masu irin wannan hali da su daina domin ba hali bane mai kyau

‘Yar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra Buhari, wacce take auren dan gidan shahararren mai kudin nan Indimi, ta wallafa wata magana a shafinta na Instagram, inda ta gargadi mutanen da basu da aiki sai cin mutuncin mutane.

Majiyarmu ta samu wanna labari daga legit a maganar da ta wallafa, Zahra ta bayyana cewa kawai mutum yaji baya kaunar wani, hakan yana nuni da cewa shi dan hassada ne. Ta shawarci duk mutanen da suke da irin wannan hali da suyi gaggawar neman mafita. Ta bayyana cewa ita ma ta taba tsintar kanta a wannan yanayin, sannan kuma tayi bayanin yadda ta samowa kanta mafita.

Ga abinda ‘yar gidan shugaban kasar ta rubuta:

Yau magana ta zanyi ta akan wata matsala ce da take damun mutanen mu. Na sha ganin mutane da suke cikin kadaici, jin kunya, da kuma tsana, ana mu’ammala dasu ta daban babu gaira babu dalili, na tsaya nayi tunanin akan menene yake kawo wannan matsalar. Abu daya dana gano shine hassada.

“Kunga idan mutum bai yi muku komai ba, kuma ya zama abinda kake shine kawai kaga ka kuntata mishi, to tabbas ya kamata ka binciki kanka domin kuwa kana da matsala. Muna kuma da wata dabi’a, ta idan taku bata zo daya da mutum ba, shikenan sai muyi ta neman hanyar da zamu kuntatawa juna, babu matsala idan baku jituwa da mutum, amma hakan ba yana nufin ku dinga fada ba, kayi masa magana ko yane ka kyaleshi kawai.

“Idan mutane suka tsane ka ko kuma suke son takura maka, ku fahimce ni hakan ya taba faruwa dani, akwai lokacin da mutane basu da aiki sai suga sun shiga rayuwata, karai kuwa zaka iya ci mini mutunci ka zage ni kuma babu abinda zai faru, amma kuma kada ka manta ramuwar gayya tafi ta gayya zafi. Kuma wannan abinda kayi mini ba zai saka raina ya baci ba.

“Babu dadi ko kadan idan ana yi maka irin wadannan abubuwan kafin ka saba, amma ina da wani sirri da zan fada muku idan kuna cikin irin wannan halin. Amma ku gaya mini abinda zaku yi idan wani ya takura ku ko ya tsane ku.”

A nan ne ‘yar gidan shugaban kasar ta tsaya da rubutunta, amma zamu cigaba da bibiyarta muga yadda zata kaya, ku biyo mu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?