Wednesday, 14 August 2019
Shin Da Gaske Adam A. Zango ya yi hadarin mota a Nijar ?

Home Shin Da Gaske Adam A. Zango ya yi hadarin mota a Nijar ?
Ku Tura A Social Media

Shahararren jarumin Kannywood kuma mawaki, Adam A. Zango ya yi hatsarin mota a kan hanyarsa ta dawowa daga Jamhuriyar Nijar tare da wasu abokansa kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram. Amma jarumin ya ce babu abinda ya same su sai dai motarsu ce hatsarin ya yi wa illa kamar yadda BBC ta ruwaito Zango yana yawan yin balaguro musamman lokutan bukukuwa ko shagali kamar na sallah babba da karama saboda gayyatarsa da ake yi domin yin casu.

 Duk kokarin da BBC tayi don ji ta bakinsa kan lamarin bai yi wu ba kawo yanzu saboda bai amsa wayarsa ba.

 Sai dai bayyanai a shafinsa na Instagram sun nuna cewa jarumin ya tafi Niyami, babban binrin Nijar ne don yin wasan sallah. Galibi dai a kan samu yawaitan hadurra a hanyoyin Najeriya musamman lokutan bukukuwa kamar Sallah, Kirsimeti da bikin sabuwar shekara. Masu nazarin al'amura su kan daganta hakan da rashin kyawun tituna da kuma tukin ganganci daga bangaren direbobi.

Sai dai kuma daga baya jarumi adam a zango yayi magana da bakinsa daga shafinsa instagram domin ji da kunnuwanku sai ku latsa akan wannan hoton nashi.

View this post on Instagram

A post shared by GOD MADE KING🇳🇬👑🇳🇬 (@adam_a_zango) on

Share this


Author: verified_user

0 Comments: