Wednesday, 21 August 2019
Shehu Hassan Kano Ya Zama Limamin Daidaita Sahun Kannywood

Home Shehu Hassan Kano Ya Zama Limamin Daidaita Sahun Kannywood
Ku Tura A Social Media

* Sai Masu Tarbiyya Ne Zasu Rika Fim
*Duk Wanda Ba Zai Bi Doka Ba Ya Bar Kano
*Fada Da Batanci A INTANET Ya Zama Haram
*Kowa Sai Ya Je An Tantance Shi

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

Hukumar Tace Finafinai ta jihar Kano karkashin jagorancin Shugabanta Isma'il Afakallahu ya rantsar da kwamitin tsoffin 'yan fim da zasu tantance duk masu ruwa da tsaki a harkar fim din Hausa.

Kwamitin da Shehu Hassan Kano ke jagoranta zai fara aikin tantancewar ne ranar Litinin mai Zuwa zai kuma dauki tsawon wata guda yana aikin tantancewar.

A tattaunawar da yayi da Jaridar #SARAUNIYA Shehu Hassan Kano ya bayyana manufar kwamitin shine tsaftace harkar fim din Hausa da marasa manufa da TARBIYYA suka cika shi da badala maimakon basira da gogewa.

Ya kuma jaddada kudirinsu na cewar ana son samar da nagartattun masana ne harkar domin dawo da martabar masana'antar kamar yadda take a baya.

Bugu da kari tare da rage kwaranyowar mata 'yan kama waje-zauna da suka mamaye harkar fim ba tare da sun zo da muharramansu su ba. Kazalika kwamitin zai rika ladabtar da masu zagi gami da batanci a kafar sadarwa.

Tantancewar ta hada da Marubuta, Masu Daukar Hoto, Masu Tace Hoto, Masu Shiryawa, Masu Bayar Da Umarni, Mawaka Da Makada, Masu Daukar Nauyi, Masu Kwalliya Da Sauransu.

Ga Cikakkiyar hirar a nan ga mai BUKATA


Share this


Author: verified_user

1 comment: