Wasanni

Paul pogba Ya Mayarwa Wadanda Suke nunamai Wariyar Launin Fata Martani Mai Zafi

Bayan cin zarafin da aka mai da nuna wariyar launin fata sanadiyyar barar da bugun daga kai sai me tsaron gida da yayi a wasan da Manchester United ta buga kunnen doki da kungiyar Wolves,Pogba ya mayarwa da wanda suka mai zagin wariyar launin fata martani.

Pogba ya dauki hoto rike da danshi kusa da hotunan marigayi mahaifinshi, Fassou Antoine da Martin Luther King inda ya bayyana cewa masu mai zagin nuna wariyar launin fata jahilci ne ke damunsu kuma hakan bazai kashe mai karfin gwiwa ba, iyaye da kakanni sun yi faftuka dan bakar fata ya samu ‘yanci dan haka shima zai ci gaba da wannan fafutuka dan masu zuwa nan gaba su samu karin ‘yanci.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *Back to top button