Friday, 2 August 2019
Nijeriya Za Ta Yi Sallah Rana Daya Da Saudiyya

Home Nijeriya Za Ta Yi Sallah Rana Daya Da Saudiyya
Ku Tura A Social Media

Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto

Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ta  ayyana yau Juma'a 2/8/2019 a matsayin daya ga watan Zulhijja 1440, inda za a yi hawan Arfa ranar Asabar 9 ga watan Zuljihha, a yi sallah babba 10 ga wata kwana daya ga hawan Arfa.

A wata takarda da Shugaban kwamitin duba wata, Farfesa Sambo Junaidu ya sanyawa hannu, kuma RARIYA ta samu kwafin, ta bayyana cewa bayan tuntubar malamai da masana da shugabannin kungiyoyin addini musulunci, kwamitin da ke baiwa Sarkin musulmi shawara akan lamurran Addini, kwamitin ganin wata na kasa da kwamitin fatawa na kasa, sun baiwa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Saad Abubakar, shawarar yau Juma'a ta kasance daya ga wata, inda Sarkin ya amince kuma ya ayyana yau a matsayin daya ga watan.

Tuni dai ita ma kasar Saudiyya ta ayyana ranar Asabar a matsayin ranar hawan Arfa da yin sallah ranar Lahadi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: