Monday, 26 August 2019
Nafi kowa Yin Fim Akan Addini, Amma malamai Basu Taba Yaba Min Ba - Adam A Zango

Home Nafi kowa Yin Fim Akan Addini, Amma malamai Basu Taba Yaba Min Ba - Adam A Zango
Ku Tura A Social Media
Tsohon jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango ya bayyana cewa mutane hudu ne suka Musulunta a sanadiyar fim dinsa na ahlul Kitabi.

Zango ya bayyana cewa tunda aka kafa masana’antar Kannywood babu wani jarumi da ya yi fina-finan fadakarwa tare da kira zuwa ga addinin Musulunci kamar shi.

Jarumin ya bayyana cewa duk da wannan kokari da yayi babu wani malami da ya taba kiransa ya bashi lambar yabo koda na katako ne, sai dai zagi da hantara.

Yace: “Mutane 4 ne suka musulunta sanadin Film dina na ahlul kitabi. Kazalika tunda aka kirkiro Kannywood babu wani jarumi dayayi fina finan Fadakarwa tare da kira akan tafarkin Addinin Islama kamarni Adam A Zango.

“Amma duk da wannan kokari da muke yi, babu wani Malamin addini da ya kiramu ya bamu koda lambar yabon katako! Sai zagi da neman Kuskurar da kokarin da muke yi.”

Adam A. Zango yayi wannan jawabin ne a yayin da ake hira da shi ta musamman domin mayar da martani ga labarin da ke dadewa bazuwa a kafafen yanar gizo mai cewa ya daura dammara wajen lalata yaran mutane mata bayan ‘yan kwanaki kadan da soma gasarsa na neman mata wadanda za su fito cikin wata sabuwar fim nasa.


Ga bidiyon nan kasa ku kalla.

View this post on Instagram

A post shared by KANNYWOOD_PAPARAZY (@kannywood_paparazy) on

Share this


Author: verified_user

0 Comments: