Monday, 12 August 2019
Manchester United ta janyo wa Frank Lampard bakin jini a Chelsea

Home Manchester United ta janyo wa Frank Lampard bakin jini a Chelsea
Ku Tura A Social Media
Ba wannan ne karon farko ba a cikin makwannin da suka gabata da aka kaddamar da maudu'in neman a kori Lampard a Chelsea a Twitter.

Maudu'in #LampardOut a Twitter da aka kaddamar ya ja hankali bayan Manchester United ta doke Chelsea ci 4-0 a wasan gasar Premier na farko da aka soma a kakar bana.
Tun a watan Yuli aka fara kaddamar da maudu'in bayan wasan Lampard na farko a matsayin kocin Chelsea bayan ya gaza doke Bohemians ta Ireland a wasan share faken kaka.


Wannan ne sakamako mafi muni a tarihin Chelsea a Old Trafford tun 1965. Kuma sakamako mafi muni ga sabon koci a tarihin Premier tun Gustavo Poyet na Sunderland ya sha kashi 4-0 a Swansea a watan Oktoban 2013.
Kuma wannan ne karon farko da kocin Chelsea ya sha kashi mafi muni a wasan shi na farko tun zamanin Danny Blanchflower da Middlesbrough ta doke 7-2 a 1978.

Sai dai Chelsea ta fi yawan taba kwallo a wasan, kuma ta fi kai hare-hare da daukar kwana.
Kuma Chelsea da aka haramtawa sayen 'yan wasa, ta fara wasan ne da matasa kamar Mason Mount da Tammy Abraham da kuma Andreas Christensen.

Frank Lampard ya ce yana ganin bai kamata ace an doke Chelsea ba, amma ya ce wannan darasi ne inda ya amsa cewa Chelsea ta tafka kura-kurai a Old Trafford.

A ranar Laraba ne kuma Chelsea da ta lashe Europa za ta hadu da Liverpool a wasan lashe Super Cup na Turai a Istanbul, kafin ta hadu da Leicester a ranar Lahadi a Stamford Bridge.
Wasu na ganin babban kalubalen da ke gaban Lampard, shi ne haduwar Chelsea da sauran manyan kungiyoyin Ingila kamar Manchester City da Liverpool da Arsenal da kuma Tottenham.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: