Friday, 23 August 2019
Malamin Addinin Musulunci Dr.Zakir Naik Ba Dan Ta'adda Bane

Home Malamin Addinin Musulunci Dr.Zakir Naik Ba Dan Ta'adda Bane
Ku Tura A Social Media


Gwamnatin Kasar Malaysia ta kama shahararren Malamin addinin Musulunci Dr Zakir Naikh kwararren Likita 'dan Kasar India wanda ya shahara wajen tafka muhawara da manyan malaman addinan Yahudu, Kiristanci, Buddah, Masu bautar shanu, Gumaka da sauransu

A wannan karnin, babu Malamin da yayi sanadiyyar musuluntar da miliyoyin mutanen duniya wadanda ba musulmai ba zuwa cikin addinin musulunci fiye da Dr Zakir Naikh

Wannan yana daga cikin dalilan da yasa gwamnatin Indiya wanda mafi yawancinsu bautar shanu suke, suka sakashi a gaba da sharri da batanci, sun jefeshi da kalmar ta'addanci, sannan sukayi barazanar kamashi, dole ya gudu daga Kasar, gwamnatin Saudiyyah ta bashi mafaka

To kwanakin baya ya koma Kasar Malaysia, ya gabatar da wata lecture kamar yadda ya saba, a cikin darasin da ya gabatar yayi magana dangane da irin tsananin kiyayya ga Musulunci da ake nuna musu a gwamnatin Kasar India

To shine mahukuntan Kasar Malaysia sukace wai wannan kalma da ya furta kokarin tunzura al'ummah da haddasa yaki da fitina tsakanin tsirarun kabilu da suke zaune a Kasar, sunce wai kalmomi ne na ta'addanci, sai suka bada umarni aka kamashi, yanzu haka yana daure ana tuhumarsa, kuma akwai yiwuwar zasu mikashi ga hannun gwamnatin India

Kama Malaman addinin Musulunci, da dauresu, da kisansu tafarkin bayin Allah na kwarai ne, kuma Sunnar Annabawan Allah ne, da manyan Malaman addinin Musulunci tun daga na farkonsu har zuwa yau, misali da Sheikhul Islam Ahmad Abdul-Haleem Ibnu Taimiyyah, shi kam a kurkuku ya mutu

Muna rokon Allah Mai iko da Buwaya akan Komai Ya kubutar mana da Dr Zakir Naikh daga hannun AZZALUMAI makiya addinin Allah

Daga Datti Assalafiy

Share this


Author: verified_user

0 Comments: