Sunday, 4 August 2019
Kashe kudi a neman 'yammata ya fi kashe kudi a kan sayen kadara muhimmanci - Jarumin Fim

Home Kashe kudi a neman 'yammata ya fi kashe kudi a kan sayen kadara muhimmanci - Jarumin Fim
Ku Tura A Social Media

Wani dattijon jarumin Fim a kasar Ghana, Oboy Siki, ya bayyana cewa kashe kudi wajen neman 'yammata ya fi kashe kudi a kan sayen kadarori amfani.

Jarumi Siki ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shi da kafar yada labarai ta ZionFelix.

Siki ya kafe a kan ra'ayin cewa kashe kudi wajen neman 'yammata ya fi muhimmanci a kan kashe kudi domin sayen kadarori, saboda mutum ba zai tafi kabari da kadara ko daya ba.

Kazalika ya bayyana cewa ya fito daga manema mata kuma zai tabbbatar da cewa bai bawa danginsa kunya ba, a saboda haka zai cigaba da kashe kudi wajen neman mata.

Ya kara da cewa, " duk da ina tsufa yanzu, zan cigaba da kashe kudina wajen kwanciya da kananan 'yammata ."

A kwanakin baya ne jarumi Siki ya bayyana cewa ya kwanta da 'yammata fiye da 2500 wanda yanzu haka yana da sunayensu a cikin kundinsa.

Majiyarmu ta wallafa labarin da jarumi Oboy Siki ya bayyana wani boyayyen lamari game da rayuwarsa, inda ya bayyana cewa yayi zina da sama da mata dubu biyu da dari biyar a rayuwarsa.

A cewar fitaccen jarumin, ya ce yana matukar son yara mata kanana, kuma idan har yace bai son kananan 'yan mata ya yiwa kanshi karya ne.

Oboy Siki wanda yayi hira da manema labarai, ya bayyana cewa neman mata yana jikinshi ne, domin kuwa mahaifinsa ma mazinaci ne, saboda haka yana matukar son mata.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: