Kannywood

Jaruman da suka fita Daga masana’antar Kannywood Sun Fara Dana sanin fita – Jarumi Ty Shaba

– Jarumi TY Sha’aban ya bayyana cewa duka jaruman da suka fita daga masana’antar Kannywood sun fara dana sanin fita

– Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin da suka gabata Jarumi Adam A. Zango da Mustapha Naburaska sun bayyana cewa sun bar masana’antar Kannywood

– Jaruman sun bayyana hakan ne saboda kama darakta Sunusi Oscar 442 da shugaban hukumar tace fina-finai yasa aka yi

Duk wanda yake bibiyar abubuwan da suka shafi masana’antar Kannywood ya san cewa an sha wata badakala a ‘yan kwanakin nan da suka wuce.

Badakalar da aka sha din kuwa ita ce maganar kama wani babban mai bada umarni a cikin fina-finan Hausa wato darakta Sunusi Oscar 442 da shugaban tace fina-finai Isma’ila na Abba Afakallahu yayi, wanda maganar ta hautsina masana’antar Kannywood din gaba daya.

Legit ta ruwaito ,Ida ba a manta ba a sakamakon wannan hukunci da shugaban hukumar yayi, sai da ta kai wasu suka fice daga masana’antar, domin nuna rashin jin dadinsu da wannan hukunci.

Daga cikin jaruman da kwashe kayansu suka fice daga wannan masana’anta, akwai Jarumi Adam A. Zango da kuma Jarumi Mustapha Naburaska.

Wannan labari na dana sanin da jaruman suke yi, ya fito daga bakin wani tsohon dan wasan wato TY Sha’aban.

Jarumi TY Sha’aban ya bayyana hakane a wani shiri na gidan rediyon Rahma dake jihar Kano, a cikin wani mai suna karkade kunnuwa.

Ga dai abinda jarumin ya ce:

Wannan abu da suka yi ba abu bane mai dadi, saboda su kansu wadanda suka fita, ina da rahotanni da nake samu daga na kusa dasu da ke nuna cewa suna dana sanin abinda suka yi.”

Shaba ya cigaba da cewa “Kannywood ita ce ta yi muku riga da wando, duk wanda aka gani a cikin harkar fina-finan Hausa, babu wanda yazo da jarin naira daya.

Jarumin ya nuna bacin ransa akan wannan lamari inda daga karshe yake bawa jaruman da suka fice daga masana’antar shawarar cewa ya kamata su dawo domin a hada karfi da karfe wajen cimma masana’antar gaba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button