Sunday, 25 August 2019
Hadiza Gabon tayi Mallam Abba Potiskum goma ta arziki bisa ibtila’in ambaliya

Home Hadiza Gabon tayi Mallam Abba Potiskum goma ta arziki bisa ibtila’in ambaliya
Ku Tura A Social Media


Jaruma a masana’antar Kannywood, Hadiza Gabon, ta aike da sakon gudunmawa ga mutumin nan da hotunansa suke ta yawo a kafafen sadarwa na zamani, Malam Abba Potiskum, bisa lalurar ambaliyar ruwa da ta afka masa a gidansa dake garin Potiskum.


Ita dai Hadiza Gabon, ta samu labarin wannan ibtila’i ne daga wajen wani bawan Allah da ya tura mata da labarin a Twitter, ita kuma ta nemi tabbaci akan labarin, sannan bayan ta tabbatar sai ta taimaka masa.


Majiyarmu ta samu daga aminchi24news, Hadiza Gabon ta taimakawa Mallam Abba da zunzurutun kudi har Naira dubu hamsin (50,000). Kuma ta aike musu da kudin ne ta Account din wata mata mai suna FATIMA IBRAHIM, wadda itace take karbar taimakon a madadin Mallam Abba da iyalansa.


Dama Hadiza Gabon ta shahara da taimakawa bayin Allah mabukata kamar Marayu, yan gudun hijira da makamantansu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: