Wednesday, 28 August 2019
Hadiza Gabon Na sake ginawa Tsohonnan da Ruwa Ya cinyewa Gida a Yobe Gidan nashi

Home Hadiza Gabon Na sake ginawa Tsohonnan da Ruwa Ya cinyewa Gida a Yobe Gidan nashi
Ku Tura A Social Media

Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon wadda kuma ta shahara wajan bayar da taimako ga marasa galihu ta taimaki tsohonnan da hotunanshi suka watsu sosai a shafukan sada zumunta bayan da ruwa ya rabashi da muhallinshi.

Taimakon da Hadiza Gabon ta wa Abba Babuga dake Fataskum jihar Yobe shine sake gina mai gidanshi da ruwa ya cinye.

Shafin gidauniyar Hadiza Gabon din na Instagram ya wallafa hotunan yanda tuni aka fara aikin sake ginawa Abba Babuga gidanshi da ruwa ya cinye.

Muna fatan Allah ya saka mata da Alheri

Share this


Author: verified_user

0 Comments: