Thursday, 1 August 2019
Gwamnatin tarayya ta tsamo ‘yan Najeriya miliyan 5 daga matsanancin talauci a shekara 3 – Buhari

Home Gwamnatin tarayya ta tsamo ‘yan Najeriya miliyan 5 daga matsanancin talauci a shekara 3 – Buhari
Ku Tura A Social Media
-Shugaba Buhari ya fadi adadin mutanen da gwamnatinsa ta tsamo daga halin matsanancin talauci a Najeriya

-Shugaban Najeriya wanda Boss Mustapha ya wakilta a wurin taron Kungiyar ILO ya ce mutum miliyan biyar gwamnatin tarayya ta fitar daga talauci a shekara uku

-Shirin N-Power ne silar tsamo mutanen daga matsanancin talauci saboda ya samar da ayyuka miliyan biyu a cewar Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shirin NSIP da gwamnatin tarayya ta fitar ya taimaka wajen ciro ‘yan Najeriya miliyan biyar daga cikin halin matsanancin talauci.

Buhari ya fadi wannan maganar ne a wurin bude taron samar da ayyuka ga matasa na duniya wanda Kungiyar Kwadago ta Duniya wato International Labour Organization (ILO) ta shirya ranar Alhamis a birnin Abuja.

Shugaban kasan ya ce wannan taro ne mai muhimmanci wanda zai taimakawa matasa su tattauna matsalar da ta shafi yadda za a daidaita tattalin arziki.

Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a wurin taron ya jinjinama ILO na mayar da hankalinta kan samar da ayyuka ga matasa.

Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya na biye da yadda abubuwa suka sauya a fadin duniyar nan a yanzu musamman a fagen ayyuka.

Muna sa ne da cewa rashin aikin yi ga matasa ya zama ruwan dare mai game duniya, domin ko wace kasa na fama da irin wannan matsalar.

“ A don haka ne ya sanya gwamnatinmu ta kara zage dantse wajen ganin ta samawa matasa aikin yi a kasar nan. Daga shekarar 2017 zuwa 2020 muna nan da tsarin farfado da tattalin arziki na musamman wato Economic Recovery Growth Plan (ERGP).

“ A karkashin wannan tsarin ne muka fitar da shirin N-Power wanda ya samar da ayyuka miliyan 2 kuma ya tsamo mutane akalla miliyan 5 daga cikin halin matsanancin talauci.” A cewar Buhari.

Haka zalika, wasu bangarorin da Shugaban kasa yayi magana a kai wadanda ke cikin tsarin farfado da tattalin arzikin sun hada da harkar noma, ma’adanan kasa da kuma Babban bankin Najeriya CBN.

® Legit

Share this


Author: verified_user

0 Comments: