Wednesday, 28 August 2019
Fariya: Wani Dan Najeriya ya yi wa diyarsa shimfida Da Bandiran Takardun Dalar Amurka (Bidiyo)

Home Fariya: Wani Dan Najeriya ya yi wa diyarsa shimfida Da Bandiran Takardun Dalar Amurka (Bidiyo)
Ku Tura A Social Media
Bayyanar wani faifan bidiyo na wani mutum dan kabilar Igbo da ya yi wa diyarsa shimfida da takardun kudi na Dalar Amurka ya jawo barkewar cece-kuce da martani daban-daban daga wurin 'yan Najeriya.

A faifan bidiyon, wanda Lauretta Onochie, hadimar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta yada a shafinta na Tuwita, an ga mutumin na fada wa diyarsa jaririya cewa ta taka takardun da ya shimfida.

Mutumin na magana ne cikin harshen Igbo a faifan bidiyon.

A cewar mutumin, "ki taka takardun kudi, ki kwanta a kan takardun kudi, ina da makudan kudi".

Mutumin ya bayyana cewa a baya kudi sun wahalar da shi amma yanzu kudi ba matsalarsa ba ne.


Ita da kan ta Onochie ta nuna bacin ran ta a kan faifan bidiyon tare da bayyana abinda mutumin ya yi a matsayin 'hauka'.

Kalli faifan bidiyon a kasa.


Wasu daga cikin masu martani a kan faifan bidiyon sun bayyana cewa ganin dan kabilar Igbo ya aikata hakan ba abin mamaki bane, saboda ko a cikin makon nan sai da hukumar bincike a kasar Amurka (FBI) ta kama wasu 'yan Najeriya 17, yawancinsu 'yan kabilar Igbo, da laifin damfarar Amurka wa.

Yanzu haka gwamnatin Amurka ta bayar da umarnin rufe hanyoyin aiko kudi daga bankunan kasar zuwa Najeriya bayan ta gano yadda bata gari daga cikin 'yan Najeriya a kasar ke damfarar mutanenta makudan kudi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: