Labarai

EFCC: An samu dankara-dankaran motoci 21 a gidan Abdulaziz Yari

-Hukumar EFCC ta kai samame gidan tsohon gwamnan Jihar Zamfara Abudlaziz Yari -Jami’ai 15 ne suka fita aikin inda suka samu dankara-dankaran motoci guda 21 a cikin gidan nasa

 -Tuni hukumar ta aikawa gwamnan da goron gayyata cewa ya zo ofishinta domin amsa tambayoyi Hukumar yaki da cin hanci da kuma yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC ta kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari dake Talata Mafara. A lokacin samamen hukumar EFCC ta samu motaci manya-manya na alfarma har guda 21.

Kamar yadda jaridar The Nation ta kawo mana za’a binciki Yari ya akayi ya mallaki wadannan motocin.

Haka zalika, EFCC ta bai wa tsohon gwamnan goron gayyata inda take sa ran ya bayyana a ofishinta domin amsa wasu ‘yan tambayoyi. Akwai manyan laifuka uku da ake tuhumar gwamnan da aikatawa na farko shi ne, N19bn kudin Paris Club da ba a san inda suka shiga ba, N35bn da aka kashewa ‘yan gudun hijira wato IDPs, Ecological Stabilization Fund da kuma isalin N151bn na ayyukan da ake cigaba da yi. Jami’an hukumar EFCC 15 ne suka kai wannan samamen a Talata Mafara inda gidan tsohon gwamnan yake. Tun shekarar 2017 hukumar ta EFCC ke bibiyar gwamnan amma sai dai a wancan lokacin yana da kariya ta musamman kasancewarsa gwamnan jiha.

Majiyar The Nation ta fitar da wani zancen hukumar EFFC mai cewa: “ Wannan kutse da EFCC tayi na shiga gidan Yari na da nasaba da bincike da mu keyi a kansa tun shekara biyu da suka wuce. Akwai matsalar da muke bukatarsa ya warware a gabanmu.

 “ Dukkanin tuhumar da muke masa ta shafi mulkinsa ne, ba wai muna kokarin kakaba masa laifi bane, amma dai muna da bukatar ya zo ofishinmu domin amsa wasu ‘yan tambayoyi.” A cewar hukumar ta EFCC.

® Legit

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button