Tuesday, 20 August 2019
Da duminsa: Zan fito takarar gwamnan jihar Kano a 2023 - Nazir M Ahmad (Sarkin Waka)

Home Da duminsa: Zan fito takarar gwamnan jihar Kano a 2023 - Nazir M Ahmad (Sarkin Waka)
Ku Tura A Social Media
Fitaccen mawakin nan na jihar Kano wanda Sarki Muhammadu Sanusi ya yiwa sarautar Sarkin Waka wato Nazir M Ahmad ya fito ya bayyana wani kudurinsa

- Fitaccen mawakin ya fito ya bayyana cewa zai fito takarar gwamnan jihar Kano a shekarar 2023 idan Allah ya kaimu

- Sai dai kuma mawakin bai bayyana ko a wacce jam'iyya yake da shirin fitowa takarar ba, yayin da yake bayanin hakan a shafinsa na Instagram

Majiyar jaridar Najeriya Hausa ta shafin Facebook, ta bakin wakilinta Ibrahim Musa Tiyagas dake jihar Kano ta bayyana cewa, shahararren mawakin nan na jihar Kano, wanda kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya bai wa sarautar Sarkin waka wato Nazir M Ahmad, ya sha alwashin fitowa takarar kujerar gwamna a jihar Kano a shekarar 2023.

Sai dai kuma shahararen mawakin Nazir M Ahmad, bai bayyana ko a wacce jam'iyya yake da shirin fitowa takarar ba.


Bugu daa kari fitaccen mawakin ya bayyana wannan aniyar ta shi ta tsaya takarar gwamnan jihar ta Kano a shafinsa na Instagram, a inda yayi bayani a cikin wani bidiyo tare da kuma bayyana ra'ayinsa.

Idan ba a manta ba satin da ya gabata mun kawo muku rahoton yadda gwamnatin jihar Kano ta kama babban daraktan masana'antar Kannywood Sunusi Oscar 442, inda wannan kamashi din ya dinga karawa sama hazo a shafukan sada zumunta.

Sannan kuma wannan kamashi din da aka yi yaso raba kan kungiyar fina-finan Hausan ta Kannywood, inda wasu ke ganin an sanya munafurci a lamarin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: