Monday, 12 August 2019
An samu karuwa: Fatima Aliko Dangote Ta Haihu A kasar Amurka

Home An samu karuwa: Fatima Aliko Dangote Ta Haihu A kasar Amurka
Ku Tura A Social Media
Mun samu labari cewa ‘Diyar babban Mai kudin Najeriya Aliko Dangote watau Fatima Dangote, ta samu karuwa inda ta haifi jaririya. Jaridar The Cable ta rahoto wannan labari 12 ga Agusta, 2019.

 Da alamu an yi wannan haihuwa ne a cikin ‘yan kwanakin nan inda labarin ya fara ratsa gari a farkon makon nan. Hakan na zuwa ne kusan bayan shekara guda da rabi da a ka yi aurensu.

Majiyarmu ta samu daga legithausa, Fatima Dangote ta bar Najeriya ne zuwa Amurka a karshen makon da ya wuce. Dangote ta haihu ne a kasar wajen. Sahibin Mijin na ta wani babban Matukin jirgin sama ne wanda ya shahara. Hajiya Dangote ta na auren Jamilu Abubakar ne wanda Mahaifinsa ya taba riken mukamin babban Sufetan ‘yan sanda a Najeriya. Jamilu shi ne babban Yaron Muhammad
D. Abubakar


Fatima da Halima su na cikin ‘Ya ‘yan Dangote. Attajirin ya na matukar Kaunar wadannan ‘Ya ‘ya na sa kamar yadda ya bayyana a ranar auren Fatima da Jamilu wanda ya ce ya dauka tamkar 'Da. A lokacin da a ka yi auren na su, Mai kudin Duniya, Bill Gates ya samu zuwa, haka kuma shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo da Attajirin nan na Nahiyar Afrika, Mo Ibrahim sun zo. Manyan ‘yan siyasan gida da su ka halarci bikin da a ka yi a bara sun hada shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bukola Saraki, Yakubu Dogara. Sarakuna irin su Rilwan Akiolu, sun halarta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: