Sunday, 4 August 2019
Amaryar Sakin Kano Sanusi II Ta Tare Bayan Shekara Hudu Da Daurin Aure

Home Amaryar Sakin Kano Sanusi II Ta Tare Bayan Shekara Hudu Da Daurin Aure
Ku Tura A Social Media

Daga El-Hajeej Hotoro Maje

Amaryar Mai Martaba Sarkin Kano,  Muhammadu Sanusi II (Wacce ita ce ta hudu) ta tare bayan Shekara hudu da daurin Aure.

An kawo Amarya Gimbiya Sa’adatu Barkindo Mustapha  fadar Sarki ranar Asabar yayin da aka yi budar-Kai ranar Lahadi.

Amaryar ba ta dade da kammala jami'a ba a Landan jim kadan bayan an daura auren.

Idan za a iya tunawa Sarki Sanusi II ya auri 'yar Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo-Musdafa, a yanayin auren da ba a yi gagarumin shagali ba gami da tara mutane ba a garin Yola, ranar 25 ga Satumbar 2015.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: