Friday, 16 August 2019
Allah ya sanya alkhairi: Fitacciyar mawakiya Maryam Sangandale za ta amarce

Home Allah ya sanya alkhairi: Fitacciyar mawakiya Maryam Sangandale za ta amarce
Ku Tura A Social Media
Fitacciyar mawakiyar arewacin Najeriya Maryam Sangandale za ta yi aure a karshen wannan watan da muke ciki

- Mawakiyar ta wallafa sanarwar hakan ne a shafinta na Facebook, inda ta gayyaci 'yan uwa da abokan arziki

- Maryam dai ta samu lambar yabo kala-kala a bangaren manyan mawaka mata na arewacin Najeriya

Fitacciyar mawakiyar nan ta arewacin Najeriya, wacce har yanzu tauraruwarta ke haskawa, Maryam A Baba, wacce aka fi sani da suna Maryam Sangandale ta gama shiri tsaf don amarcewa da angonta a ranar 28 ga wannan wata na Agusta shekarar 2019.

Mawakiyar ta wallafa sanarwar daurin auren nata ne a shafin sada zumunta na zamani na Facebook, inda ta gayyaci masoyanta, 'yan uwa da abokan arziki dake lungu da sako na kasar nan zuwa wajen daurin auren.Source :legit

Maryam A Baba dai mawakiya ce da ta yi suna sosai a arewacin Najeriya, inda take wakoki kala-kala a bangaren fina-finan Hausa, biki, siyasa da dai sauransu.

Maryam ta karbi lambar yabo kala-kala a bangaren zakakuran mawaka mata na arewacin Najeriya. Babbar wakar da tayi wacce ta sanya ta yi suna ita ce 'Sangandale', inda dalilin wakar ne yasa aka canja mata suna zuwa Maryam Sangandale.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: