Monday, 12 August 2019
A Cikin Kowace Tawaga Ba Rasa Bayin Allah Na Kwarai Sadiq Sani Sadiq Yayi Abin Mamaki

Home A Cikin Kowace Tawaga Ba Rasa Bayin Allah Na Kwarai Sadiq Sani Sadiq Yayi Abin Mamaki
Ku Tura A Social Media


Daga Datti Assalafiy

Wannan da kuke gani sunansa Sadik Sani Sadik, fitaccen jarumin 'dan wasan kwaikwayo na hausa, yau kusan kwanaki 10 yana birnin Maiduguri jihar Borno, kullun tare da shi ake gabatar da sallah ta asuba a Masallacin Indimi dake  Damboa Road.

Na'ibin limamin dake jan sallah na asuba a Masallacin na Indimi Ustaz Mustapha Muhammad Bakomi ya kirani a waya ya sanar dani, yace Sadik Sani Sadiki ya bashi mamaki matuka, kullun tare dashi ake sallah na asuba, idan an idar da sallah baya barin masallacin, zai cigaba da yin akzar da sauran Zikiri har sai rana ta bayyana sosai ya gabatar da sallah ta walaha kafin ya fita daga masallacin.

Hakika cikin kowace irin jama'a ko tawaga na al'ummar musulmi ba'a rasa bayin Allah na kwarai a cikinsu, ya kamata mu dinga sara muna duban bakin gatari, kar muje mu dinga taba bayin Allah na kwarai.

Ko a harkan wasan kwaikwayo da suke, Sadik Sani Sadik da Ali Nuhu ni dai ban taba jin wani mummunan al'amari daga garesu ba, suna da kokari wajen kiyayewa gwargwadon abinda ya bayyana garemu, ina ganin kimarsu sosai.

Allah Ka kara albarka wa rayuwar Sadik Sani Sadik.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: